Hukuncin Kotu Ya Ƙara Rikirkita Jam'iyyar NNPP, Tsagin Kwankwaso Ya Yi Magana

Hukuncin Kotu Ya Ƙara Rikirkita Jam'iyyar NNPP, Tsagin Kwankwaso Ya Yi Magana

  • Tsagin NNPP da ke goyon bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya jaddada cewa har yanzu shugabancin jam'iyya na hannunsa
  • Mai magana da yawun NNPP na tsagin Kwankwaso, Ladipo Johnson ya ce hukuncin da kotun Abuja ta yanke bai canza tsarin shugabanci ba
  • Tun bayan zaɓen 2023, NNPP ta dare gida biyu, ɓangare ɗaya na tare da Kwankwaso yayin da ɗaya ɓamgaren ke goyon bayan Boniface Aniebonam

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Dr. Ajuji Ahmed, bangaren da ke biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso, ta nanata cewa shugabancin jam'iyya na hannunta.

Tsagin Kwankwaso ya ce har yanzu shi ke rike da ikon tafiyar da NNPP duk da hukuncin da kotu ta yanke kwanan nan dangane da rikicin shugabancin jam'iyyar.

Kwankwaso.
Tsagin Kwankwaso ya jaddada cewa shugabancin NNPP na hannunsa Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Daily Trust ta ce tun bayan zaɓen 2023, NNPP ta fada cikin rikicin cikin gida da ya janyo rabuwar kai tsakanin bangarori biyu da ke ikirarin mallakar jam’iyyar.

Kara karanta wannan

2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane hukunci kotu ta yi kan rikicin NNPP?

A makon da ya gabata, wata babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da ƙarar da bangaren Rabiu Kwankwaso ya shigar.

Wannan ƙara ta kalubalanci halascin bangaren Dr. Boniface Aniebonam da Shugaban jam’iyya na ƙasa, Dr. Agbo Major, wanda ke ikirarin shugabancin NNPP.

Wadanda suka shigar da ƙarar sun hada da Dr. Ajuji Ahmed da wasu mutum 20 waɗanda duk ƴan tsagin Kwankwaso ne.

Sun bukaci kotu ta hana waɗanda ake tuhuma gudanar da taruka ko gangami ko kuma jagorantar babban taron NNPP na ƙasa, bisa hujjar cewa an kore su daga jam’iyyar tuni.

Sai dai Alkalin, kotun, Mai Shari’a M.A. Hassan, ya ce kotu ba ta da hurumin sauraron irin wannan ƙara.

A cewar alkalin irin wadannan matsaloli suna cikin harkokin cikin gida na jam’iyya wanda dokar kasa ta haramta wa kotuna shiga, sai dai idan matsalar ta shafi zaɓe ko ɗan takara.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Shugaban jam'iyyar APC ya rasu cikin yanayin ban al'ajabi

“Kotu ba ta da hurumi kan rikicin shugabanci ko na mambobi a jam’iyya, sai dai batun zaben ‘yan takara ne kadai,” in ji Mai Shari’a Hassan.

Hukuncin kotu ya kara rikita jam'iyyar NNPP

Wannan hukunci bai fayyace wanda ke kan shugabanci ba, lamarin da ya sake zurfafa rikicin da ya raba jam’iyyar NNPP gida biyu, rahoton Punch.

Bangaren Aniebonam ya fassara hukuncin a matsayin amincewa da shugabancinsu, yayin da bangaren Ajuji ya ce kotu kawai ta ce ba za ta saurari ƙarar ba, amma ba ta soke ko canza tsarin shugabanci na yanzu ba.

A martaninsa, bangaren Kwankwaso ya gargadi jama’a da kada su bari a yaudare su da fassarar da ya kira “ƙarya” daga bangaren da aka riga aka kore daga jam’iyyar.

NNPP.
NNPP ta kara fadawa wani rikicin kan hukuncin babbar kotun tarayya Hoto: Ajuji ahmed
Asali: Twitter

Da gaske an kwace NNPP daga hannun Kwankwaso?

Mai magana da yawun NNPP Ajuji, Barista Ladipo Johnson, ya ce:

"Abin mamaki waɗanda muka kai ƙara kotu, korarrun ƴan jam'iyya sun yi gaggawar fitowa suna yaudarar jama'a da fassarar hukunci wacce ba ta dace ba kwata-kwata.

Kara karanta wannan

'Kotu ta kori Kwankwasiyya?' Jam'iyyar NNPP ta fayyace hukuncin kotu

"Kotun ba ta ce su ne shugabanni ba. Ba ta bayar da wani sabon umarni ga INEC ko canjin shugabanci ba."

Ya kara da cewa hukuncin da Kotun Tarayya ta yanke a ranar 18 ga Afrilu, 2024, ya tabbatar da korar Aniebonam, Agbo, Olaposi da sauran mambobinsu daga NNPP, kuma har yanzu babu wata kotu da ta soke wannan hukunci.

NNPP ta samu karuwa a Kano

A wani labarin, kun ji cewa Kwankwaso ya sake karɓar rukunin magoya bayan APC da suka sauya sheka zuwa NNPP a karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Wannan dai wata alama ce ɗa ke nuna yadda Kanawa ke kara gamsuwa da jam'iyyar NNPP mai mulki a cewar Sanata Kwankwaso.

Bugu da ƙari, Jagoran na NNPP ya samu halartar taron shagalin Sallah na ƴan Kwankwasiyya karo na bakwai tare da manyan jiga-jigan jam’iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel