"Ba Mai So": Gwamna Ya Tuna baya, Ya Fadi Yadda APC Ta Roke Shi Ya Yi Takara a 2023

"Ba Mai So": Gwamna Ya Tuna baya, Ya Fadi Yadda APC Ta Roke Shi Ya Yi Takara a 2023

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya tuna baya kan yadda ya yi takarar sanata a zaɓen shekarar 2023
  • Monday Okpebholo ya bayyana cewa jam'iyyar ta lallaɓa shi domin ya yi takarar sanatan Edo ta Tsakiya a ƙarƙashin inuwarta
  • Gwamnan ya bayyana cewa a lokacin hankalin mutane ya fi karkata wajen neman tikitin takara a ƙarƙashin jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayyana yadda jam’iyyar APC ta roƙe shi domin ya tsaya takara a zaɓen 2023.

Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa APC ta roƙe shi kan ya tsaya takarar kujerar Sanatan Edo ta Tsakiya a zaɓen gama gari na shekarar 2023, duk da cewa bai da sha’awar shiga siyasa.

Gwamna Monday Okpebholo
Monday Okpebholo ya ce APC ta roki ya yi takara a 2023 Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Facebook

Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar Leadership.

Kara karanta wannan

An fayyace shirin Peter Obi na 'hadewa' da El Rufai a jam'iyyar SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda APC ta lallaɓi Okpebholo ya yi takara

Tsohon sanatan ya ba da labarin yadda aka lallaɓa shi ya amince da tsayawa takara sakamakon rashin masu sha’awar jaraba sa'arsu wajen neman kujerar a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC.

"Idan ka kalle ni da kyau, ba ni da yawan magana. Ban taɓa sha’awar siyasa ba. Amma ina so na ga garin da na fito ya ci gaba."
"Hakan ne abin da ke raina, kuma wannan ne ya ba ni ƙarfin gwiwa. Babu wanda ya so ya tsaya takarar Sanata a ƙarƙashin APC, amma suna faɗa da kashe juna don samun tikitin takarar kujerar majalisar dokoki a PDP."

- Gwamna Monday Okpebholo

Gwamnan ya ƙara da bayyana cewa tsayawarsa takara ya auku ne sakamakon haɗin gwiwar manyan jiga-jigan jam’iyyar ne.

“Mutane uku ne suka shigo gidana suka ce, ‘Mun zo ne domin mu gaya maka ka tsaya takarar Sanata.’"

- Gwamna Monday Okpebholo

Kara karanta wannan

Ta tabbata Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP? An samu bayanai

Gwamna Okpebholo ya bayyana yadda ake kallon shi a baya a matsayin wanda ba zai iya ba, amma yanzu ya zama babban ginshikin siyasa a yankin.

Ya ce abubuwa da dama sun sauya tun bayan da ya samu nasara, kuma jama’a da dama da suke a PDP suna komawa APC saboda ganin gaskiyar manufofinta da cigaban da take kawowa.

Gwamna Monday Okpebholo
Monday Okpebholo ya yi takarar sanata a karkashin jam'iyyar APC a 2023 Hoto: @m_akpakomiza
Asali: Facebook

Gwamna Okpebholo ya hango sauyi a Kudu maso Kudu

Gwamnan ya yi hasashen cewa za a samu manyan sauye-sauyen siyasa a yankin Kudu-Maso-Kudu.

Ya ce akwai alamun haɗa kai da manufofin cigaban gwamnatin tarayya, wanda zai kawo sauyi mai ma’ana ga rayuwar al’umma.

A cewarsa, yanzu APC tana ƙara samun ƙarfi a yankin Kudu maso Kudu saboda abubuwan da suka faru a baya da kuma nasarorin da aka samu ƙarƙashin mulkin jam’iyyar.

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaɓen gwamnan Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jiɓar Edo, ta zartar da hukunci kan ƙarar da jam'iyyar AA ta shigar.

Kara karanta wannan

Kisan 'yan Arewa a Edo: Rundunar sojoji ta bayyana yadda aka warware matsalar

Jam'iyyar wace ke cikin jam'iyyun da suka fafata a zaɓen, ta shigar da ita nr domin a soke nasarar da Gwamna Monday Okpebjolo ya samu.

Kotun mai alƙalai guda uku ta yi watsi da ƙarar wacce ta ƙalubalanci nasarar da Gwamna Monday ya yi a zaɓen na shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng