‘Ba Ni ba Neman Sanata’: Gwamna Ya ce Yana Gama Wa’adinsa Zai Yi Ritaya a Siyasa

‘Ba Ni ba Neman Sanata’: Gwamna Ya ce Yana Gama Wa’adinsa Zai Yi Ritaya a Siyasa

  • Gwamnan Abia, Alex Otti, ya ce ba zai nemi kujerar Sanata ba bayan karewar wa'adinsa a 2031
  • Otti ya ce yana son ya bar matasa su samu dama su mulki da jagoranci a Najeriya saboda lokaci ya yi
  • Alex Otti ya yi alkawarin daukar matakan gyara domin adalci da daidaito ga kowa da ke cikin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya yi magana kan jita-jitar da ake yadawa cewa zai nemi kujerar sanata bayan kammala mulkinsa.

Gwamna Otti ya fayyace cewa ba ya da niyyar tsayawa takarar Sanata bayan karewar wa'adinsa na mulki.

Gwamna ya kore jita-jitar neman sanata bayan kammala mulki
Gwamna Alex Otti ya ce ba zai nemi kujerar sanata ba bayan kammala wa'adinsa a Abia. Hoto: Alex Otti.
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu kan makomar siyasarsa

Otti ya bayyana haka ne ranar Asabar 5 ga watan Afrilun 2025 a lokacin taron karbar bakuncin da kungiyar cigaban Anambra reshen Aba ta shirya masa, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

'Ka sani mulki zai kare,' An yi wa Tinubu nasiha mai zafi kan tafiya Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya musanta rade-radin da ke yawo cewa zai tsaya takarar Sanata, yana mai cewa hakan ba gaskiya ba ne kwata-kwata.

Alex Otti ya bayyana bukatar ba matasa damar shugabanci saboda yadda al'umma ke sauyawa tare da karuwar fitowar matasa.

Ya ce:

"Lokacin da na kammala shekara takwas a nan, zan yi ritaya, ba zan tafi birnin Abuja ba, ina rokon jama'a ku daina yada karya.
"Ba mu da kuruciya sosai yanzu, al'umma na canzawa, matasa na tasowa, Lokaci ne da za mu ba su dama."

Haka kuma, Otti ya bayyana shirin gwamnati na sake duba batun korar ma’aikata 154 da aka yi a 2011, mafi yawansu malamai ne.

Ya ce zai umarci shugaban ma’aikatan jihar da ya duba batun cikin gaggawa domin ganin an yi adalci da gyara matsalar.

Otti ya ce ana iya dawo da wadanda shekarunsu basu kai 65 ba ta hanyar kwangila saboda karancin malamai a jihar.

Kara karanta wannan

'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka

Ya bayyana cewa kora ma’aikatan saboda asalin jiharsu ba gaskiya ba ce kuma doka ba ta yarda da hakan ba.

Ya ce:

"Ga wadanda shekarunsu suka wuce, gwamnati za ta nemo hanyar da ta dace wajen biya musu diyya."
Gwamna ya bukaci ba matasa dama a mulki
Gwamna Alex Otti ya kora jita-jitar cewa zai nemi sanata bayan kammala mulki. Hoto: Alex Otti.
Asali: Facebook

Alwashin gwamna Otti ga al'ummar jiharsa

Gwamna Otti ya tabbatar wa jama'a cewa gwamnatin sa za ta tsaya kan gaskiya, adalci, da gyara barnar gwamnatoci da suka gabata.

A jawabansu daban-daban, dan majalisa Stephen Ucheonye da Chief Obiora Nwakpadolo sun yabawa jagorancin Gwamna Otti.

Sun ce ayyukan da gwamnan ke yi ne ya sa suka shirya taron karbar bakuncin domin girmamawa da godiya gare shi.

Gwamna ya yi wa sarakunan gargajiya gata a Abia

Kun ji cewa Gwamnatin Abia ta fara biyan karin albashi daga N250,000 zuwa N350,000 duk wata ga sarakunan gargajiya na jihar.

Gwamnatin ta shirya sake fasalin tsarin ci gaban jihar na shekaru 30 don ya yi dai dai da yanayin tattalin da ake ciki yanzu.

Gwamna Alex Otti ya dauki matakai masu tsauri kan kasuwanci a kan tituna da kuma tukin hannu daya don rage hadurra.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.