Gwamna Ya Samu Nasara, Ya Zama Ɗan Takara a Inuwar Jam'iyyar APGA
- Gwamna Soludo ya samu nasarar lashe zaɓen fidda gwani na ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APGA a zaɓe mai zuwa
- Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta watau INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamnan Anambra ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025
- Da yake jawabi bayan samun nasara, Gwamna Soludo ya ce duk nasarorin da gwamnatinsa ta samu bai taɓa karɓo bashin ko kwabo ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo ya samu nasarar lashen tikitin takara da zai ba shi damar neman tazarce a inuwar jam'iyyar APGA a zaɓen Anambra mai zuwa.
Farfesa Soludo ya samu wannan nasara ne a zaben fitar da ɗan takarar gwamna da jam'iyyarsa ta APGA ta shirya yau Asabar, 5 ga watan Afrilu, 2025.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta tataro cewa hukumar zaɓe watau INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamnan jihar Anambra ranar 8 ga watan Nuwamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APGA ta gudanar da zaben fidda gwani ne a ranar Asabar a filin Alex Ekwueme da ke Awka, inda Soludo ya kasance dan takara guda daya tilo, babu mai ja da shi.
Sakamakon zaben fidda gwanin APGA
Shugaban zaben fidda gwanin da APGA ta gudanar, Uche Nwegbo, ya bayyana cewa:
"Jimillar deleget da aka tantance su domin kada kuri’a su ne 3,175 daga cikin 3,260. Daga cikin kuri’un da aka kada, 3,172 ne sahihai, yayin da hudu ba su inganta ba.
"Gwamna Soludo ya samu kuri’u 3,168, babu wanda ya kada kuri’ar rashin amincewa da tazarcen mai girma gwamna.
"Saboda haka, bisa hurumin da doka ta bani, na ayyana Farfesa Chukwuma Soludo a matsayin dan takarar jam’iyyarmu.”
Gwamna Soludo ya yi jawabi bayan nasara
Gwamna Soludo ya karɓi wannan takara da hannu bibbiyu, yana mai gode wa jam’iyya da al’ummar jihar Anambra, Leadership ta tattaro.
"Anambra ta APGA ce, kuma APGA ta Anambra ce. Na karɓi wannan takara da zucuya ɗaya. Wannan goyon baya da kuka nuna mani ba zan taɓa manta wa ba a rayuwata,” in ji shi.

Asali: Facebook
Gwamna Soludo ya jero nasarorin da gwamnatinsa ta samu zuwa yanzu ba tare da ciwo bashi ba.
“Mun kawo sauyi mai amfani a Anambra ba tare da aro ko kwabo daya ba. Wannan somin taɓi ne kawai, Anambra ba ta ga komai ba tukuna.”
Soludo ya yaba da tsarin da aka bi yayin gudanar da zaben fidda gwani, inda ya gode wa jam’iyya, kungiyoyin magoya baya da kuma wakilan INEC.
Ya kuma bayyana cewa zai tafi da mataimakinsa na yanzu, Dr. Onyeka Ibezim, matukar ba shi ne ke da wata matsala ko uzuri ba.
Zaɓen Anambra: Ɗan takara ya bar APC
A wani labarin, kun ji cewa rikicin APC ta kara tsanani yayin da ɗan takarar gwamna ya bar jam'iyyar ana shirye-shiryen zaben fidda gwani ranar Asabar.
Paul Chukwuma ya miƙa takardar ficewa daga APC ga shugabannin jam'iyya a gunduma ta 2 da ke karamar hukumar Anambra ta Gabas.
Chukwuma ya zama ɗan takara na biyu da ya janye daga zaɓen fidda gwanin APC a jihar Anambra da ke Kudu maso Gabashin Najeriya.
Asali: Legit.ng