2027: SDP Ta Waiwayi Manyan Ƴan Adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, Ta Mika Masu Buƙata 1
- Jam'iyyar SDP ta yi kira ga manyan ƴan adawa da suka kunshi Atiku Abubakar da Peter Obi da su shigo cikinta domin ceto Najeriya
- Mataimakin shugaban SDP na Kudu maso Gabas, Arinze Ekelem ya ce jam'iyyar ta buɗe kofa ga kowane ɗan Najeriya mai kishin ƙasa
- Ekelem ya yabawa shugabananin SDP bisa kokarin da suke yi wanda a cewarsa, yanzu ƴan siyasa daga jam'iyyu daban-daban ke shigo masu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Jam'iyyar SDP ta fara zawarcin manyan jagororin ƴan adawa da jiga-jigan APC mai mulki a shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
SDP a yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga manyan ‘yan siyasa a Najeriya da su shiga jam’iyyar domin hada kai wajen samar da sabon tsarin siyasa da zai ceto kasar daga halin da take ciki.

Asali: Twitter
Daily Trust ta ce daga cikin wadanda SDP ke kira akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da dan takarar shugaban kasa na LP a 2023, Peter Obi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SDP ta buƙaci ƴan adawa su shigo cikinta
Sauran waɗanda SDP ta buƙaci su shigo cikinta sun haɗa da da tsofaffin ministoci, Rauf Aregbesola da Rotimi Amaechi, da sauran manyan ƙusoshin adawa da jiga-jigan APC.
Wannan kiran ya fito ne daga mataimakin shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa (Kudu maso Gabas), Sir Arinze Ekelem, cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a birnin Awka, Jihar Anambra.
Ekelem ya bayyana cewa jam’iyyar SDP ta samar da sabuwar dama ga ‘yan Najeriya da ke neman sauyi na gaskiya a harkar shugabanci.
"SDP jam’iyya ce da ke karfafa hadin kai da walwala ga kowa. Wuri ne ga duk wani dan Najeriya da ke neman mafitar siyasa domin ceto wannan kasa daga halin da ake ciki.
"Muna kira ga shugabannin da ke da kishin kasa da su taho su hade da mu domin gina sabuwar Najeriya.”
- In ji Arinze Ekelem.
Shugabannin SDP sun samu goyon baya
Ekelem ya kuma bayyana cikakken goyon bayan yankin Kudu maso Gabas ga shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Alhaji Shehu Musa Gabam da kwamitin gudanarwa (NWC).
Ya yabawa kokarin shugabannin SDP bisa gyara da bunkasa jam’iyyar domin fuskantar kalubale da nasarorin da ke gabanta.
Ya kara da cewa yawan shiga SDP da manyan ‘yan siyasa ke yi a sassa daban-daban na ƙasar nan alama ce ta yadda jama'a ke kara yarda da jagoranci da tsarin SDP, musamman yayin da zaben 2027 ke kara matsowa.
Kabir Abdullahi, wani ɗan PDP da ya koma SDP tun lokacin da El-Rufai ya sauya sheka ya shaida wa Legit Hausa cewa yana sa ran Atiku zai baro PDP kafin 2027.
A cewarsa, tunanin Atiku da sauran manyan adawa kamar Peter Obi za su koma SDP ne ya sa tun wuri ya bi El-Rufai.
Kabir ya ce da izinin Allah lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sake haɗa kai su canza gwamnati mai ci domin ceto kasarsu daga tuƙin ganganci.
"Lokaci kaɗai muke jira amma ina ji a raina Atiku zai dawo SDP, zamu haɗa tawagar da za ta kawo ƙarshen wannan baƙin mulkin," in ji shi.
SDP ta nesanta kanta da sauya shekar El-Rufai
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar SDP reshen jihar Kaduna ta ce har yanzun tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai bai dawo cikinta ba a hukumance.
Mataimakin Sakataren SDP na Arewa maso Yamma, Idris Inuwa, ya ce batun shigar El-Rufai cikin jam’iyyar jita-jita ce kawai da ake yaɗawa amma har yanzu ba shi da rijista.
Inuwa ya ce kwata-kwata ba su san da El-Rufai a jam'iyyar ba saboda ba mambanta ba ne har yanzu.
Asali: Legit.ng