Zaben Edo: Dan Takarar PDP zai Dauki Mataki bayan Hukuncin Kotu

Zaben Edo: Dan Takarar PDP zai Dauki Mataki bayan Hukuncin Kotu

  • 'Dan takarar PDP a takarar da ta wuce, Asue Ighodalo, ya sanar da shirin kalubalantar hukuncin kotu kan zaben Edo
  • Ighodalo ya bayyana cewa hukuncin da aka yanke babban cin amanar dimokuradiyya ne da yancin yan kasa
  • Ya bukaci magoya bayansa da su kasance cikin lumana, su guji tada zaune tsaye, kuma su ci gaba da bin doka da oda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Edo – Dan takarar PDP a zaben gwamna a jihar Edo, Asue Ighodalo, ya ce zai sake daukaka kara kan hukuncin kotu game da sakamakon zaben.

Kotun da mai shari’a Wilfred Kpochi ke jagoranta ta tabbatar da Sanata Monday Okpebholo a matsayin halastaccen gwamnan Edo a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Ka sani mulki zai kare,' An yi wa Tinubu nasiha mai zafi kan tafiya Faransa

Ighodalo
Tsohon dan takarar gwamnan PDP ya nufi kotu Hoto: Asue Ighodalo - AI Comms
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

AIT ta ruwaito cewa Asue Ighodalo ya gaggauta fitar da sanarwa, kuma ya kalubalanci hukuncin da ke tabbatar wa abokin karawarsa da nasara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta cikin wata sanarwar da ya raba wa manema labarai, Ighodalo ya kara jaddada ra'ayinsa na cewa dokar kasa tana ci gaba da zama ginshikin dimokaradiyya a Najeriya.

Dan takarar PDP a Edo zai tafi kotu

Daily Post ta wallafa cewa Asue Ighodalo ya bayyana cewa yana girmama tsarin shari’a a matsayin hanya ta ƙarshe na samun adalci ga talakawa.

Dan takarar ya ce:

"Saboda haka, na umarci tawagar lauyoyina da su garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara domin kalubalantar wannan hukunci, wanda muke ganin babban cin amanar adalci ne."

Ya kara da cewa zai ci gaba da neman adalci a wannan batu, tare da tabbatar da cewa ba a tauye hakkokin mutanen Edo na zaben shugabannin da suke son su jagorance su ba.

Ya ce:

"Wannan ba game da ni ko wani mutum ɗaya ba ne; yana da alaƙa da ainihin dimokuradiyya, kare haƙƙinmu na na zaɓen makomarmu cikin ‘yanci, da kuma gado da za mu bari ga al’ummomi masu zuwa."

Kara karanta wannan

'Ba zan yi sata ba': Ɗan majalisa ya cire tsoro a gaban ƴan mazabarsa bayan shan suka

'Dan takarar gwamna ya ba jama'a hakuri

Asue Ighodalo ya yi kira ga jama’a da su kasance cikin zaman lafiya, natsuwa da kuma bin doka bayan wannan hukuncin kotun da ya ke ganin bai yi masu dadi ba.

Tsohon
Tsohon dan takarar gwamnan Edo a PDP, Asue Ighodalo Hoto: Asue Ighodalo - AI Comms
Asali: Twitter

Ya bayyana cewa zai ci gaba da fafatukar kwato masu hakkinsu na fita zaben da kada kuri'a domin zabarsu na jagoranci jihar Edo.

Ighodalo ya ba su tabbacin cewa:

"Wannan ba ƙarshen tafiyarmu ba ne, sai dai farkon wata babbar gwagwarmaya don adalci, dimokuraɗiyya, da kuma kare amanar da jama’a suka ba ni da abokin takara na, Barr. Osarodion Ogie, a ƙarƙashin tutar jam’iyyarmu ta PDP."

Ighodalo ya jaddada cewa sun tsaya tsayin daka, sun kuduri aniyar ci gaba da fafutukar kare yancin jama'a a, kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bin gaskiya da adalci.

Edo: PDP ta yi rashin nasara a kotu

A baya, mun kawo labarin kotun sauraron kararrakin zaɓen gwamnan Edo da ke Abuja ta yi watsi da ƙarar da jam’iyyar AA ta shigar, tana neman soke zaɓen Monday Okpebholo. A hukuncin da wani kwamitin alkalai uku ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Wilfred Kpochi ya yanke, kotun ta ce ƙarar ba ta da tushe ballantana makama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.