"Barazana ga Tinubu": Za a Kafa Sabuwar Jam'iyyar Adawa, Sun Bayyana Tambarinsu

"Barazana ga Tinubu": Za a Kafa Sabuwar Jam'iyyar Adawa, Sun Bayyana Tambarinsu

  • Ƙungiyar siyasa (TNN) ta fara shirye-shiryen zama jam'iyya a Najeriya yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun TNN, Mohammed Adah Shaibu, ya fitar a Kaduna, ya ce sun miƙa bukatar zama jam'iyya ga INEC
  • Hukumar zaɓe watau INEC ta bayyana cewa ta samu sakon kungiyoyi 91 da ke son zama jam'iyyun siyasa a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wata sabuwar ƙungiyar siyasa mai suna 'Team New Nigeria (TNN)' ta sanar da shirinta na neman rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.

TNN ta bayyana cewa za ta nemi Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta mata rijistar zama halastacciyar jam'iyya bayan cika dukkan sharuddan da ake buƙata.

TNN da shugaban INEC.
TNN, ta nemi rajistar zama halastacciyar jam’iyya a INEC Hoto: @Inecnigeria
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa a baya-bayan nan, INEC ta tabbatar da karɓar buƙatu daban-daban guda 91 na sabbabin jam’iyyun siyasa da ke neman rajista.

Kara karanta wannan

APC: Jiga-jigan PDP sun fitar da matsaya kan kawancen jam'iyyu gabanin 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

TNN ta bayyana tambari da manufa

A wata sanarwa da kakakin TNN, Mohammed Adah Shaibu, ya fitar a Kaduna, ƙungiyar ta bayyana sabon tambarinta na zama jam'iyyar siyasa.

Mohammed Adah ya ƙara da cewa kwamitin zartarwa (NEC) na TNN da Majalisar Amintattu (BoT) sun amince da tambarin jam’iyyar.

Haka zalika ya ce sun amince da manufofi da taken TNN, kuma sun ƙaddamar da gajerun kalmomin da za a riƙa amfani da su wajen bayyana jam’iyyar.

“Da wannan ci gaba da muka samu, ya zama shi ne farkon tafiyarmu ta ƙoƙarin gina sabuwar Najeriya da muke mafarki.
"Sunanmu shi ne TNN, taken mu kuwa shi ne ‘Gina Nigeria’, yayin da manufarmu ta kasance ‘Haɗa kai da gina ƙasa," in ji shi.

TNN za ta kadddamar da kundin tsarin mulki

Sanarwar ta ƙara da cewa tsarin mulki da manufofin TNN za a ƙaddamar da su a hukumance a watan Afrilu 2025 yayin taron ƙasa da za a gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan siyasar Najeriya ke rububin sauya jam'iyya gabanin zaben 2027

Shugaban ƙungiyar, Modibbo Yakubu Farakwai, ya tabbatar da cewa sun bi dukkan hanyoyin da INEC ta gindaya don rajistar jam’iyya.

INEC.
Kungiyar TNN ta fara shirim.zama jam'iyyar siyasa Hoto: @inecnigeria
Asali: UGC

A cikin shirin da take yi don tabbatar da samun rajista, TNN ta kafa kwamitoci masu muhimmanci, ciki har da Kwamitin Shari’a da Bin Doka, wanda Farfesa Muhammad Zakari Yaro ke jagoranta.

Ta kuma kafa Kwamitin Gudanar da Siyasa, wanda Farfesa Silva Opuala-Charles ke shugabanta.

Kwamitocin da jam'iyyar ta kafa

Sauran kwamitocin sun haɗa da:

Kwamitin Hulɗa da Ƙungiyoyi da Jama’a – Alhaji Omar Yusuf Aiyelabegan (Shugaba)

Kwamitin Kula da Kuɗi – Dr Adebayo Akin-Omotuyi (Shugaba)

Kwamitin Yaɗa Labarai – Dr Mohammed Adah Shaibu (Shugaba)

Kwamitin Tsarin Ƙungiya – Farfesa Iheanacho Agboti (Shugaba)

Kwamitin Shirye-shirye – Farfesa Waziri Garba Dahiru (Shugaba)

Kwamitin Rajista da Daidaita Membobi – Sanata Ibrahim Muhammad (Shugaba)

Sanarwar ta ƙara da cewa waɗannan kwamitocin sun kammala aikinsu kamar yadda aka tsara, wanda hakan ya ƙara ƙarfafa shirin samun rajistar jam’iyya.

Kara karanta wannan

Ana shirin haɗaka don kayar da Tinubu, ƴar majalisar tarayya ta fice daga YPP

Jam’iyyun adawa ba su da karfin canza komai

Sai dai, a siyasance jam’iyyun adawa a Najeriya sun kasance kamar masu sharhi ne kawai ba tare da ikon aiwatar da sauyi ba.

Duk da yawan sukar da suke yi wa gwamnati, rashin hadin kai da karancin tasiri a cikin tsarin mulki na hana su cimma wani gagarumin sauyi.

Jam’iyyun adawa na fuskantar matsaloli da dama da suka hada da rashin tsayayyen tsari, rashin hadin kai tsakanin shugabanninsu, da kuma yawan rikicin cikin gida. Wannan ya hana su kasancewa abar dogaro wajen kawo sauyi mai ma’ana.

Bugu da ƙari, tsarin siyasan Najeriya na bai wa jam’iyya mai mulki cikakken iko, wanda hakan ke hana adawa samun wata dama ta gaske.

Misali, mafi yawan ‘yan majalisa suna cikin jam’iyya mai mulki, kuma da zarar an samu sabani, sau da yawa suna komawa wurin gwamnati mai ci domin kare muradunsu.

Kara karanta wannan

Shugabannin SDP sun ziyarci mai martaba sarki, ya tsage masu gaskiya kan yaudarar jama'a

Sanata Suleiman ya koma SDP

A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban PDP, Sanata Suleiman Mohammed Nazif, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP.

An ce Sanata Nazif ya dauki wannan matakin ne domin tabbatar da aniyarsa ta yi wa al’umma hidima fiye da bukatun siyasa na kashin kansa.

Salisu Ibrahim ya fadada labarin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262