'Ka Sani Mulki zai Kare,' An Yi wa Tinubu Nasiha Mai Zafi kan Tafiya Faransa

'Ka Sani Mulki zai Kare,' An Yi wa Tinubu Nasiha Mai Zafi kan Tafiya Faransa

  • Bode George ya soki Bola Tinubu bisa tafiyarsa Faransa a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalar tsaro
  • Ya ce gwamnati na aiwatar da manufofi masu barazana ga hadin kan kasa, tana maimaita kura-kuran baya
  • George ya kuma zargi APC da Majalisar Dattawa da kokarin kawo cikas wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa, Olabode George, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu bisa tafiyarsa Faransa.

Bode George ya ce bai kamata shugaban Najeriya ya bar kasar ba a daidai lokacin da ake fama da matsaloli da dama.

Bode George
An soki Tinubu kan tafiya Faransa ana fama da matsaloli a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga|Bode George
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa Bode George ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba mai taken "Ina Najeriya ta dosa?"

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ke fuskantar barazanar rugujewa saboda manufofin gwamnati da rashin daukar matakai masu kyau.

“Najeriya na fuskantar barazanar rugujewa”

Bode George ya ce gwamnatin APC na maimaita kura-kuran da suka haddasa rugujewar Jamhuriyya ta farko da ta biyu.

A karkashin haka ya yi gargadi da cewa idan ba a dauki mataki ba, Najeriya na iya fadawa cikin matsala mai girman gaske.

"Idan mu ka kalli tarihi, irin wannan yanayi ne ya haddasa yakin duniya na biyu lokacin da Adolf Hitler na Jamus da Benito Mussolini na Italiya suka haddasa rikici a duniya.
"Amma a karshe, aka tashi tsaye aka ceci duniya,"

- Bode George

Tribune ta wallafa cewa ya kara da cewa:

"Yanzu haka Najeriya na cikin matsalolin tsaro, yunwa, da rashin ayyukan yi, amma Bola Tinubu ya bar kasar zuwa Paris, Faransa, ba tare da wani dalili bayyananne ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan Sokoto ya yi magana da babbar murya kan kisan 'yan Arewa a Edo

George ya ce idan aka kalli manufofin gwamnatin APC, yana da sauki a fahimci cewa shugabanni ba sa jin ra’ayoyin ‘yan kasa, kuma suna aiwatar da manufofi masu barazana ga hadin kan kasa.

Tinubu
Tinubu zai shafe mako 2 a Faransa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Zargin watsi da matsalolin Najeriya

Bode George ya ce duk da yadda ‘yan Najeriya ke cikin tsaka mai wuya, gwamnati da majalisa sun fi mayar da hankali kan dawo da Sanata Natasha maimakon magance matsalolin kasa.

"Ina mamakin yadda APC da majalisa suka fi damuwa da maganar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, maimakon matsalolin tsaro da yunwa da ke addabar ‘yan kasa.
"Wannan abin kunya ne!"

In ji George

Ya zargi majalisar dattawa da nuna bangaranci a kan lamarin Natasha, yana mai cewa abin da ke faruwa a kanta wata alama ce ta yadda Najeriya ke kara tabarbarewa a idon duniya.

Magana kan dakatar da Fubara a Rivers

Bode George ya kuma zargi APC da kokarin kutsawa siyasar Jihar Rivers ta hanyoyin da ba bisa ka’ida ba.

Kara karanta wannan

An fara bugawa kan kudirin hana Tinubu, Atiku da Obi takara a 2027

George ya ce:

"Ana kokarin kiranye wa Natasha daga majalisa ta kowace hanya, sannan kuma ana kokarin kwace mulki a Jihar Rivers ta hanyar kutse. Wannan babban kuskure ne,"

Bode George ya gargadi Tinubu da shugabannin gwamnati cewa mulki ba na dindindin ba ne, don haka su tuna cewa duk wata matsala da suka haddasa, su ne za su fuskance ta a gaba.

Kisan Edo: APC ta bukaci kama 'yan PDP

A wani rahoton, kun ji cewa APC ta zargi PDP ta jawo rikici a Uromi da ya haddasa kashe Hausawa matafiya 16.

Biyo bayan faruwar lamarin, APC ta bukaci jami'an tsaro su kama shugabannin PDP a jihar Edo kan zarginsu da kawo rikici a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng