'Ana Neman a Sanya Dokar Ta Baci a Edo kan Kisan Hausawa,' Jam'iyyar APC
- Jam'iyyar APC ta zargi PDP da shirya tayar da tarzoma domin Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Edo
- Rikicin siyasa a Edo ya ƙara kamari tsakanin PDP da APC bayan wasu mutane sun kashe Hausawa 16 a kan hanya
- APC ta bukaci jami’an tsaro su kama shugabannin PDP bisa zargin haddasa rikici domin kawo rudani a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Edo - Jam’iyyar APC ta zargi PDP da ƙoƙarin tayar da fitina a Edo domin haddasa rikici da kawo dokar ta-baci a jihar.
Shugaban APC a Edo, Hon. Jarret Tenebe, ya bayyana haka ne a taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata, 1 ga Afrilu, 2025.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da tashar AIT ta wallafa a X, Hon. Jarret Tenebe ya ce PDP da abokan tafiyarta na ƙoƙarin jefa jihar cikin hargitsi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce PDP na fatan ganin Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Edo saboda rashin kwarin gwiwar lashe shari’ar kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamna.
Kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamna a Edo ta yanke hukunci kan ƙarar da PDP da dan takararta, Chief Asue Ighodalo, suka shigar kan nasarar Gwamna Monday Okpebholo na APC.
PDP da ɗan takararta sun kalubalanci hukuncin INEC na ayyana Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Edo da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba, 2024.
APC ta bukaci kama shugabannin PDP
Hon. Tenebe ya zargi PDP da haddasa rikici a jihar, yana mai cewa jam’iyyar na aiki da wasu tubabbun jami’an tsaron ESN domin tayar da tarzoma a yankunan kamar Uromi.
Ya yi zargin cewa PDP ce ta haddasa rikicin Uromi, inda ya ce rashin jin daɗin jam’iyyar kan ziyarar Gwamna Okpebholo ga iyalan waɗanda suka rasu a Kano ya tabbatar da hakan.
Saboda haka, APC ta bukaci jami’an tsaro su kama shugabannin PDP a Edo domin dakile shirinsu na tayar da zaune tsaye a jihar.

Asali: Facebook
“Za mu koka ga kasashen waje” – APC
APC ta ce za ta rubuta ƙorafi ga jakadun ƙasashen waje da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin a dawo da waɗanda ke ƙoƙarin tayar da rikici a Edo domin su fuskanci shari’a.
“Muna kira ga ƙasashen waje da su taimaka wajen dawo da waɗanda ke tunzura mutane su aikata ta’addanci a Edo.
"Jama’ar Edo sun zaɓi wanda suke so, kuma ba za mu bari a murƙushe wannan zaɓi da dabaru marasa kyau ba,”
- Hon. Tenebe
Edo: Iyalan Hausawan da aka kashe sun magantu
A wani rahoton, kun ji cewa iyalan Hausawan da aka kashe a Edo sun bayyana yadda suka rika magana da 'yan uwansu ana kokarin kashe su.
'Yan uwan mamatan sun bayyana cewa sun kirasu a waya a lokacin da aka fara kai musu hari, kuma sun bukaci a musu adalci.
Asali: Legit.ng