Duk da Kwararan Matakai a Kogi, Masoyan Natasha Sun Yi Mata Tarbar Girma a Jirgi
- Magoya bayan Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce ke wakiltar Kogi Tsakiya a majalisar dattawa, sun fito domin tarbar ta a ranar Talata
- Daruruwan jama'a ne suka fito domin gana wa da Sanatarsu, duk kuwa da cewa gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga a jihar
- Haka kuma gwamnatin, a karkashin Usman Ododo ta haramta duk wani taro ko gangami, bayan ta ce an samu bayanai kan rashin tsaro
- Jama’ar Kogi Tsakiya sun bijire wa umarnin, kuma daruruwan mutane suka fito dauke da kwalaye don nuna goyon bayansu ga Natasha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kogi – Magoya bayan ƴar majalisar da aka dakatar daga aiki, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, sun yi fitar dango domin tarbar ta.
Wannan na zuwa bayan gwamnatin Kogi, karkashin jagorancin Usman Ododo ta haramta duk wani nauyin taro ko gangami saboda abin da ta kira 'barazanar tsaro.'

Asali: Facebook
The Nation ta wallafa cewa, kwamishinan 'yan sanda na jihar Kogi, Miller Dantawaye, ya tabbatar da cewa duk wani gangami ya sabawa da umarnin gwamnati.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CP Dantawaye ya ci gaba da kira ga Natasha Akpoti-Uduaghan da ta soke taron Sallah da aka shirya a yankin Kogi Tsakiya.
Jama'a sun fito tarbar Sanata Natasha a Kogi
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa magoya bayan Sanata Natasha sun bijirewa umarnin gwamnati, inda daruruwa suka fito domin tarbar ta da nuna goyon baya.
Jama'ar yankin sun nuna mata kauna a lokacin da hukumar zabe ta INEC ta bayyana cewa an samu wasu daga cikin ƴan yankin sun mika mata bukatar tsige Sanatar daga majalisa.
Yunkurin yi wa Natasha kiranye ya biyo bayan dakatar da ita da majalisar dattawa ta yi mata, bisa zargin rashin da'a da take dokokin majalisa da gayya.
Yadda 'yan Kogi suka goyi bayan Natasha
Wasu mutane dauke da kwalaye sun fito suna bayyana cikakken goyon baya ga Natasha Akpoti Uduaghan, suna masu alfari da ita duk da dambarwarta da majalisa.

Asali: Facebook
Sanata Natasha, wacce majalisa ta dakatar ta samu matsala ne bayan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da nemanta da kuma cin zarafinta.
Daga cikin rubuce-rubucen goyon bayan akwai;
"Maraba da dawowa, ‘yar kasar Ebira mai daraja, al'ummar Okene gaba daya suna goyon bayanta."
'Al'ummar Adavi baki daya su na goyon bayanki.'
"Ba zan fasa taro ba," Natasha
A baya, mun wallafa cewa ofishin yada labaran Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ya fito da sanarwa game da ziyarar da Sanatar ke shirin yi a yankin Kogi Tsakiya domin bikin Sallah Karama.
A cikin wannan sanarwa, Ofishin yada labaran ta musanta rahotannin da ke cewa an soke wannan ziyara, inda ta bayyana cewa, babu wani canji ko soke wannan ziyarar da aka shirya.
Rahotanni sun fara yawo a kan cewa an soke taron bayan gwamnatin Usman Ododo ta Kogi ta sanar da haramta duk wani nau'in taro ko gangami a fadin jihar saboda barazanar tsaro.
Asali: Legit.ng