Filato: Magoya bayan PDP Sun Kone Tutar Jam’iyyar kan Tallafin Ramadan
- Magoya bayan PDP a gundumar Lamba a jihar Filato sun kone tutocin jam’iyyar yayin wata zanga-zanga a ranar Laraba
- Masu zanga-zangar sun ce an basu tallafin da bai taka kara ya karya ba, wanda suka ce bai dace da yawan magoya bayan jam’iyyar ba
- Baya ga rushe tutoci da hotunan kamfen, masu zanga-zangar sun kuma kone tallafin da aka basu, suna nuna rashin jin dadinsu
- Duk da koke-koken 'yan PDP, shugaban karamar hukumar Wase, Hamisu Amani, bai fitar da wata sanarwa ba kan wannan batu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau - A ranar Laraba ne magoya bayan PDP a gundumar Lamba da ke karamar hukumar Wase a jihar Filato sun banka wa tutocin jam’iyyar wuta.
Sun gudanar da zanga-zanga suna korafin cewa an ba su abin da bai taka kara ya karya ba da sunan tallafin azumin watan Ramadan.

Asali: Original
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun yi tattaki a tituna suna rera wakar ba ma so, kai wa shugaban karamar hukuma tallafinsa da sauran kalamai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan an gan su suna rushe tutoci da hotunan kamfen, sannan su ka banka musu wuta a kan hanya tare da kona tallafin da aka ba su.
Magoya bayan jam'iyyar PDP sun fusata
Daily Post ta ruwaito cewa masu zanga-zangar sun zargi shugaban karamar hukumar Wase da hana su tallafin da aka ware domin ‘ya’yan jam’iyyar a yankin.
Sun ce shugaban ya aika da buhuna tara na shinkafa da masara, kowanne dauke da sikeli shida, zuwa mazabar da ke da dubban magoya bayan jam’iyyar.

Asali: Twitter
Haladu Musa, daya daga cikin ‘ya’yan PDP a yankin, ya bayyana bacin ransa da cewa:

Kara karanta wannan
Jerin kura kurai 5 da musulmi ke yi a ranar ƙaramar sallah da yadda za a kauce masu
"Dubi dan tallafin da suka kawo mana a matsayin ‘ya’yan jam’iyya. Muna cikin Ramadan, amma an ba mu sikeli biyu na shinkafa da sikeli daya na masara ga rumfar Ja’oji. Haka aka ba rumfar Runji."
Ƴan jam'iyyar su na ganin bai dace jagororinsu su yi masu kyautar raini ba, ganin irin gudunmawar da suke bayar wa wajen ci gaban PDP a jihar.
Har yanzu, shugaban karamar hukumar Wase, Hamisu Amani, bai ce komai a kan zargin da 'yan jam'iyyarsa ke yi ba.
"Ana yaɗa jita-jita kan Atiku," Ƙusa a PDP
A baya, mun wallafa cewa shugaban hadakar PDP na kasa, Dr. Emeka Kalu, ya fito fili ya na yin Allah-wadai da jita-jitar da ke yawo kan Atiku Abubakar da gwamnan Legas.
Ana yaɗa cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ba Atiku Abubakar tallafin kudi don yakin neman zabe, lamarin da Dr. Kalu ya ce abu ne mai kamar wuya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Dr. Kalu ya bayyana wannan batu a matsayin makirci da nufin bata wa Atiku suna, wanda ya ce hakan ba zai hana shi neman a gyara Najeriya ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng