Shugaban Hadakar PDP Ya Yi Allah Wadai da Jita Jitar da ake Yada wa kan Atiku

Shugaban Hadakar PDP Ya Yi Allah Wadai da Jita Jitar da ake Yada wa kan Atiku

  • Shugaban hadakar PDP na Kasa, Dr. Emeka Kalu, ya yi Allah wadai da rahoton da ke cewa Atiku Abubakar ya nemi tallafin kudi daga gwamnan Legas
  • Dr. Kalu ya ce abin mamaki ne, yadda wasu za su yi tunanin tsohon shugaban kasar nan zai nemi tallafin kudi daga gwamnatin Babajide Sanwo Olu
  • Ya kara da cewa Atiku Abubakar bai taba dogaro da kudi daga 'yan adawa da sauran 'yan siyasa wajen neman takarar shugaban kasa da yake yi ba
  • Ya yi kira ga jam’iyyar APC da ta maida hankali kan inganta shugabanci maimakon yin kokarin dora alhakin gazawar gwamnati kan shugabannin adawa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Shugaban hadakar PDP na Kasa, Dr. Emeka Kalu, ya yi Allah wadai da abin da ya kira jita-jita marasa tushe da makama da ake yadawa kan Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi martani ga Amurka kan zargin kashe kiristoci karkashin Tinubu

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Legas, Dr. Kalu ya yi watsi da labarin cewa gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya ba Atiku tallafin kudi don yakin neman zabensa na baya.

Atiku
An soki masu adawa da Atiku Abubakar Hoto: Babajide Sanwo Olu/Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Kalu ya bayyana cewa matukar akwai alamun rashin tunani, idan har wani zai yi tunanin Atiku Abubakar zai nemi tallafin kudi a wajen Sanwo Olu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin bata wa Atiku Abubakar suna

Dr. Emeka Kalu ya bayyana wadannan zarge-zarge a matsayin makarkashiya don bata suna tare da jaddada cewa Atiku Abubakar bai taba dogaro da tallafin kudi daga jami’an gwamnati don yakin neman zabe ba.

Ya ce:

"A tarihinsa na siyasa, Atiku bai taba dogaro da wani tallafin kudi daga masu rike da mukaman gwamnati ba. Dole ne a kawo karshen wadannan rahotanni na kage da nufin bata masa suna."

Dr. Kalu ya kalubalanci wadanda ke yada wadannan ikirari da su gabatar da kwakkwaran hujja da ke tabbatar da zargin da suke yi.

Kara karanta wannan

Da gaske Atiku ya karbi miliyoyin Naira daga Gwamnan Legas a lokacin zaben 2023?

'Ana yi wa Atiku zagon kasa'

Shugaban hadakar PDP ya bayyana cikakken yakinin cewa duk irin wadannan karairayi ba za su hana Atiku Abubakar ci gaba da fafutukar ganin an samu ingantacciyar shugabanci ba.

Atiku
Tsohon dan takarar shugaban kasa Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Depositphotos

Emeka Kalu ya kara da cewa:

"Abin mamaki ne yadda wani zai yi tunanin cewa Atiku zai nemi taimakon kudi daga gwamna da ke tare da abokan hamayyarsa a siyasa.
Atiku mutum ne mai jajircewa da kyakkyawan tsari, wanda ya dukufa wajen ganin an samu Najeriya mai ingantacciyar siyasa da ci gaba."

Ya bukaci jam’iyyar mai mulki da ta mayar da hankali kan magance matsalolin shugabanci maimakon kokarin dora alhakin gazawarta kan shugabannin adawa irinsu Atiku Abubakar.

Kalaman Atiku sun jawo masa magana

A wani labarin, kun ji cewa APC reshen jihar Akwa Ibom ta yi martani mai zafi kan zargin da Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya yi wa shugaban majalisar dattawa.

Tsohon dan takarar PDP ya zargi Godswill Akpabio da cin hanci, lamarin da daraktan yaɗa labaran jam'iyyar, Otuekong Iniobong John, ya ce Atiku ba shi da hurumin fadin haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.