"Sai Mun Tashi Tsaye," Gwamnan APC Ya Hango Damuwa a Zaben 2027
- Shugaban gwamnonin APC, Hope Uzodinma, ya bayyana cewa akwai bukatar manyan jam’iyyar su tashi tsaye domin ƙarfafa ta
- Gwamnan ya bayyana haka ne a taron liyafar buɗe baki da cin abincin 'Lent' da ya shirya ga Musulmi da Kiristocin jam’iyyar a Abuja
- Sanata Uzodinma ya ce duk da jam’iyyar APC na da gwamnonin jihohi 21 da kuma rinjaye a majalisar tarayya, ka da a yi sake da zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, ya bukaci takwarorinsa, sauran jami’an da aka zaɓa, da jiga-jigan jam’iyyar su dage wajen tallata ta.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a taron bude baki na musamman hadi da liyarfar 'lent' da ƙungiyar ta shirya a Abuja domin tattauna batutuwan da ke gaban jam’iyyar kafin zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnonin jihohin Ekiti, Ondo, Edo, da Ebonyi sun halarci taron, tare da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da mataimakinsa Barau Jibrin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran manyan da suka halarci taron sun haɗa da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, wasu daga cikin 'yan majalisa masu ci da kuma tsofaffin ‘yan majalisa, da manyan shugabanni a APC.
Uzodinma ya bayyana dalilin taron APC
AIT ta ruwaito cewa Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa an shirya taron ne domin haɗa shugabannin jam’iyyar da ke rike da mukamai a matakin ƙasa da jihohi domin tattauna hanyoyin cigaban ƙasa makomar APC.
Ya ƙara da cewa taron ya ba da dama ga shugabanni su yi addu’a domin haɗin kan ƙasa da cigaban Najeriya gaba ɗaya.
A cewarsa:
"Nasarar wannan gwamnati nasararmu ce gaba ɗaya. Dukkanmu wakilai ne na tallata wannan gwamnati da jam’iyya, kuma dole mu ɗauki nauyin kare ta."
"Dole ne mu yi aiki tukuru domin cigaban wannan gwamnati mu kuma yi alfahari da ita, saboda mu APC ne, kuma dole ne mu nuna ƙaunar jam’iyyarmu."
‘Kar ku tsorata,’ Gwamna ga ‘yan APC
Gwamna Uzodinma ya bayyana cewa kasancewar APC na da gwamnonin jihohi 21 da kuma rinjaye a majalisar dokokin ƙasa, bai kamata su damu da tasirin jam’iyyun adawa ba.
Ya gode wa sauran 'yan jam’iyyar bisa goyon baya da haɗin kan da suke bai wa Shugaba Bola Tinubu da gwamnatinsa.

Asali: Facebook
Uzodinma ya ce gwamnatin APC na tafiya a kan hanya madaidaiciya ta hanyar aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki da ke haifar da sakamako mai kyau.
Gwamnan ya ce:
"Muna kan hanyar da ta dace, kuma ana samun nasara daga matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta rayuwar ‘yan Najeriya,."
Jam'iyyar APC ta fara shirin zaben 2027
A wani labarin, mun ruwaito cewa akwai alamun cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da yawancin ‘yan majalisar tarayya da ke kan tutar APC za su samu tikitin tazarce a 2027.
Majiyoyi daga cikin APC sun bayyana cewa wannan mataki na bayar da tikitin tazarce yunkuri ne na tabbatar da ikon Bola Tinubu a kan tsare-tsaren jam’iyyar da dakile barazana.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng