Halin da Ake ciki a Rivers bayan Shugaban Riko Ya Hau Kujerar Fubara

Halin da Ake ciki a Rivers bayan Shugaban Riko Ya Hau Kujerar Fubara

  • Sabon shugaban mulkin rikon kwarya na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas (ritaya), ya isa Fatakwal domin fara aiki
  • Ya gana da tawagar gwamnatin tarayya, jami’an gwamnatin jihar da manyan hafsoshin tsaro a gidan gwamnati
  • Ibok-Ete Ekwe Ibas ya ce zai mayar da hankali kan dawo da zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a Ribas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Sabon shugaban mulkin rikon kwarya na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas (ritaya), ya isa Fatakwal domin karɓar ragamar jagorancin jihar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shi ne bayan ayyana dokar ta-baci a jihar sakamakon rikicin siyasa da ya yi tsanani.

Rivers
Shugaban riko ya fara aiki a Rivers. Hoto: Imran Muhammad
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa bayan rantsar da shi a ranar Laraba, Ibas ya bayyana shirin sa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Kara karanta wannan

Ribas: An fallasa yadda Wike da gwamnatin Tinubu suka kitsa dakatar da Fubara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibas ya isa jihar Rivers domin fara aiki

Sabon shugaban mulkin rikon kwarya na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas, ya isa filin jirgin saman kasa da kasa na Fatakwal, da misalin karfe 11:30 na safe.

Bayan isarsa, ya wuce kai tsaye zuwa gidan gwamnatin jihar, a nan jami’an gwamnati suka tarbe shi cikin girmamawa da shirin mika masa ragamar mulki.

A ranar Talata ne shugaba Bola Tinubu ya bayyana dokar ta-baci a Ribas, tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Ngozi Odu, da ‘yan majalisar dokokin jihar.

Wannan matakin na Tinubu ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan siyasa da kungiyoyin farar hula, inda da dama suka ce hakan ya saba doka.

Taron sirri da manyan jami’ai a Rivers

Bayan isarsa, sabon shugaban mulkin rikon kwaryar ya jagoranci wani taron sirri a zauren zartaswa na gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da mutanen Buhari sun tunkari Tinubu da murya daya

Taron ya samu halartar tawagar gwamnatin tarayya, jami’an tsaro da kuma manyan jami’an gwamnatin jihar.

Bayan kammala taron, Ibas ya shaida wa manema labarai cewa babban aikin sa shi ne dawo da zaman lafiya da tabbatar da doka da oda a jihar.

Tun da aka rantsar da shi a fadar shugaban kasa ya jaddada cewa zai yi aiki tare da hukumomi a jihar.

Hoton Fubara na nan daram a gidan gwamnati

Daily Trust ta wallafa cewa a lokacin da Ibas ke kaddamar da aikinsa a gidan gwamnati, an gano hoton Gwamna Siminalayi Fubara yana nan daram a bango.

Hakazalika, hoton shugaba Bola Tinubu na nan a zauren taron, sai dai ba a tabbatar da cewa ko hoton Fubara zai cigaba da kasancewa a fadar gwamnatin ba.

A yanzu haka dai za a zuba ido aga salon da sabon shugaban rikon kwaryar zai dauka wajen tafiyar da lamuran mullki a jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martanin barazanar dakatar da shi kamar yadda aka yi a Ribas

Fubara
Gwamnan Rivers da aka dakatar. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Asali: Facebook

Fubara: Gwamnoni sun kalubalanci Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Kudu maso Kudu sun kalubalanci shugaban kasa Bola Tinubu kan dakatar da Simi Fubara.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnonin sun bukaci dawo da gwamnan jihar da sauran wadanda shugaban kasar ya dakatar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel