'Za Ku Ga Karshen Su,' El Rufa'i Ya Yi Allah Ya Isa ga 'Yan Majalisar Kaduna
- Rahotanni na nuni da cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce majalisar jihar ba ta da hurumin bincikensa
- Nasir Ahmed El-Rufa'i ya ce an sauke shugaban hukumar tattara haraji ne saboda ya dage sai shugaban majalisa ya biya haraji
- Haka zalika tsohon gwamnan ya zargi Gwamna Uba Sani da karɓar kason 40% daga duk kwangila da ya bayar a jihar Kaduna
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa’i, ya mayar da martani kan binciken da majalisar dokokin jihar ke yi a kan gwamnatinsa.
Nasir El-Rufa’i ya ce ba ya tsoron shari’a, kuma duk wanda ake zargi da cin hanci a gwamnatinsa sun yi Allah ya isa.

Asali: Facebook
Nasir El-Rufa'i ya yi bayanin ne a cikin wata hira da ya yi da Rediyon Freedom kan lamuran da suka shafi harkokin gwamnati da siyasa.

Kara karanta wannan
'Yadda Ribadu ya hada kai da ICPC domin kai ni kurkuku kafin zaben 2027' - El-Rufai
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hirar, tsohon gwamnan ya musanta duk wani zargi da ake masa na karɓar cin hanci daga ‘yan kwangila a lokacin mulkinsa.
El-Rufa’i ya caccaki majalisar Kaduna
Nasir El-Rufa’i ya zargi majalisar dokokin Jihar Kaduna da kokarin bata masa suna ba tare da wata hujja ba.
Tsohon gwamnan ya ce majalisar ba ta da ilimin da zai ba ta damar gudanar da bincike mai zurfi a kansa ko gwamnatinsa.
Rikicin shugaban majalisa da KADIRS
Ya kuma yi zargin cewa an sauke shugaban hukumar tattara haraji na jihar ne saboda ya dage cewa shugaban majalisar ya biya harajin da ya dace.
A cewarsa, hakan ya nuna cewa binciken da majalisar ke yi yana da wata manufa ta daban maimakon neman gaskiya.
Da ya ke barranta daga zargin da majalisar ta yi masa, El-Rufa'i ya ce:
"Mu da sauran wadanda ake zargi mun yi musu Allah ya isa, kuma za a ga yadda za su kare."

Kara karanta wannan
"40% ake ba shi," El Rufai ya zargi Uba Sani da yin kashe mu raba da ƴan kwangila
El-Rufa’i ya musanta karɓar cin hanci
El-Rufa’i ya musanta duk wani zargi da ake yi masa na karɓar cin hanci daga ‘yan kwangila a lokacin gwamnatinsa.
Tsohon gwamnan ya ce:
"Idan wani ɗan kwangila ya taba ba ni cin hanci, ya fito ya bayyana,"
Ya ce lokacin da hukumar ICPC ta gayyaci ‘yan kwangilarsu don yin bincike, babu wanda ya ce ya taba ba shi cin hanci.
A cewarsa, duk abin da ake faɗa a kansa ƙarya ce kawai da ake yi don bata masa suna saboda cimma manufar siyasa.
Zargin da El-Rufa'i ya yi wa Uba Sani
Malam Nasir El-Rufa’i ya zargi Gwamna Uba Sani da kokarin rusa shi ta hanyar amfani da binciken majalisa.
El-Rufa'i ya ce alamu sun nuna cewa gwamnan na kokarin kitsa wasu abubuwa don ya iya shafa masa kashin kaji.

Asali: Twitter
Tsohon gwamnan ya kuma zargi Uba Sani da karɓar kason 40% daga duk wata kwangila da za a bayar a jihar Kaduna.
Sheikh Gumi ya caccaki El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa ana ganin malamin addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya caccaki Nasir El-Rufa'i.
Malamin ya nuna cewa tsohon gwamnan Kaduna ya taba caccakarsa a wani taro, saboda haka shi ma zai yi amfani da damarsa wajen rama wa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng