A Karon Farko, Jam'iyyar APC Ta Ƙasa Ta Yi Maganar Sauya Shekar El Rufai zuwa SDP

A Karon Farko, Jam'iyyar APC Ta Ƙasa Ta Yi Maganar Sauya Shekar El Rufai zuwa SDP

  • Jam'iyyar APC ta kasa karkashin jagorancin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta maidawa Nasir El-Rufai martani bayan ya koma SDP
  • A wata sanarwa da kakakin APC, Felix Morka ya fitar, ya yi ikirarin cewa El-Rufai ya sauya sheka ne saboda ba a naɗa shi minista ba
  • APC ta kuma caccaki tsohon gwamnam bisa komawa SDP, tana mai cewa babu ta inda sabuwar jam'iyyarsa ta fi APC kyawawan manufofi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar APC ta ƙasa yi watsi da sukar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi mata lokacin da ya sauya sheƙa zuwa SDP.

APC ta bayyana cewa fushin Malam El-Rufai na da nasaba da rashin samun mukamin minista a gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ganduje da El-Rufai
APC ta yi ikirarin cewa El Rufai ya sauya sheƙa nw saboda haushin rasa muƙamin minista Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: Twitter

Jam'iyyar APC ta ƙasa karkashin Abdullahi Ganduje ta bayyana hakan ne a wata wata sanarwa da ta wallafa a shafin X ranar Litinin, 17 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

Siyasa mugun wasa: El Rufa'i na fatan Atiku da Obi su hade da shi a SDP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

APC ta faɗi dalilin sauya shekar El-Rufai

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun kakakin APC na ƙasa, Felix Morka, ta nuna cewa El-Rufai na ƙoƙarin sauke fushinsa kan APC ne saboda bai samu mukamin minista ba.

"El-Rufai ya rage ƙimarsa a idon jama’a, domin ya zama misalin ɗan siyasar da ke cike da son kai, girman kai, da kuma fushi wanda ke haddasa rikici a tsarin siyasa,”

- In ji Felix Morka.

Tun farko, El-Rufai ya zargi APC da bijire wa ainihin manufofinta, yana mai cewa jam’iyyar yanzu tana hannun masu son zuciya da ke neman amfanin kansu kawai.

APC ta caccaki sukar da El-Rufai ya mata

Sai dai APC ta mayar da martani da cewa El-Rufai yana jin haushi ne saboda bai samu mukamin minista a mulkin Tinubu ba.

“Ikirarin El-Rufai cewa ya fice daga APC saboda ta kauce wa manufofinta na asali ba gaskiya ba ne. Ya na ƙoƙarin amfani da wannan hujja don ɓoye haushinsa.

Kara karanta wannan

Tsofaffin ministocin Buhari 10 da manyan ƙusoshi na shirin bin El Rufai zuwa SDP

"Abin da ya dame shi kawai shi ne gaza samun mukamin minista,"

- in ji Felix Morka.

Manufofin SDP sun fi na APC ne?

Jam’iyyar APC ta kuma soki matakin El-Rufai na shiga SDP, tana mai jefa masa tambaya da cewa ko jam’iyyar da ya koma ta fi APC manufofi masu kyau?

APC ta jaddada cewa Tinubu na kokarin inganta tattalin arzikin ƙasa, tana mai cewa cire tallafin mai, daidaita canjin kuɗi, da jawo hannun jari na ƙasashen waje na daga cikin nasarorin da ya samu.

Jam'iyyar APC.
APC ta ce El-Rufai ya ji haushin hana shi mukamin minista Hoto: APC Nigeria
Asali: Getty Images
“Zargin El-Rufai cewa Tinubu ya gaza ba gaskiya ba ne. A kowane bangare, ana ganin ci gaba a kokarin wannan gwamnati na cika alkawurran da ta ɗauka a lokacin kamfe,"

- in ji APC.

Jam’iyyar ta kuma bukaci El-Rufai da ya daina yin suka mara amfani, maimakon haka ya mayar da hankalinsa kan sukar da za ta kawo gyara.

Kara karanta wannan

"Ba mu yarda ba," El Rufai ya ƙara shiga matsala bayan komawa SDP, matasa sun masa rubdugu

El-Rufai ya yi magana kan takara a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce da yiwuwar ya nemi takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

El-Rufai ya ce ya bar komai a hannun jam'iyyar SDP da sauran ƴan Najeriya, idan suka bukaci ya tsaya takara. ba shi da wani zaɓi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng