Natasha: 'Yan Siyasar Arewa Sun Huro Wuta, Suna So Shugaban Majalisa Ya Yi Murabus

Natasha: 'Yan Siyasar Arewa Sun Huro Wuta, Suna So Shugaban Majalisa Ya Yi Murabus

  • 'Yan siyasar Arewa sun bukaci Godswill Akpabio ya yi murabus domin a gudanar da bincike kan zarge-zargen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Kakakin LND, Dakta Ladan Salihu, ya ce zargin lalata da ake yiwa shugaban majalisar dattawan ya zama barazana ga mutuncin majalisar
  • A hannu daya kuma, ƙungiyar NCSON, tare da ƙungiyoyi 65 sun bukaci jama’a da su kwantar da hankali har sai an kammala bincike a majalisa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kungiyar 'yan siyasar Arewa (LND) ta tsoma baki a tirka tikar da ake tafkawa game da zargin lalata da ake yi wa shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin cewa Sanata Akpabio ya nemi ya yi lalata da ita a wani sabon gidansa.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Bauchi: 'Dan shekara 20 ya kashe mahaifiyarsa da tabarya

'Yan siyasar Arewa sun tsoma baki a takaddamar Natasha da Akpabio
'Yan siyasar Arewa sun nemi Akpabio ya yi murabus bayan zargin Sanata Natasha. Hoto: @NGRSenate, @Imranmuhdz
Source: Twitter

A martanin kungiyar LND bisa jagorancin tsohon gwamnan Kano, Mallam Ibrahim Shekarau, an nemi Akpabio da ya yi murabus daga shugabancin majalisar, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan siyasar Arewa sun nemi Akpabio ya yi murabus

'Yan siyasar na Arewa sun nuna cewa murabus ɗin Akpabio za ta nuna adalci da kuma ba da dama ga yin sahihin bincike kan zarge-zargen Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kakakin LND, Dakta Ladan Salihu, ya ce matakin zai taimaka wajen dawo da amana da kuma kare mutuncin majalisar dattawa.

Dakta Ladan, wanda tsohon dan takarar gwamnan Bauchi ne, ya ce domin tabbatar da gaskiya da adalci, ya zama dole Akpabio ya yi murabus daga mukaminsa.

'Yan kungiyar LND, sun jaddada cewa zaman Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa zai iya kawo cikas ga damar gudanar da sahihin bincike.

A cewar sanarwar Dakta Ladan, wannan batu ya zarce matsalar mutum guda, yanzu ya zama barazana ga inganci da kwarjinin majalisar dattawa a idon jama’a.

Kara karanta wannan

Ana zarginsa da neman matar aure, shugaban Majalisa ya nemi gwamna ya koma APC

Kungiyar NCSON ta nemi jama'a su yi hakuri

Kungiyar NCSON ta yi magana kan rigimar Natasha da Akpabio
Kungiyar NCSON ta nemi 'yan Najeriya su kwantar da hankali a yi bincike kan rigimar Natasha da Akpabio. Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Kungiyar LND ta bukaci a gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin, tare da bayar da shawarar cewa NHRC ko kwamitin ladabtarwa na majalisa su jagoranci binciken.

A wani bangare, wata ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa da ke ƙarƙashin inuwar NCSON, tare da haɗin guiwar ƙungiyoyi 65, ta yi kira da a kwantar da hankali kan rikicin.

Shugaban NCSON, Comrade Victor Kalu, tare da sakataren ƙungiyar, Alhaji Ali Abacha, sun bukaci al'ummar kasar du dakata da yanke hukunci har sai an kammala bincike.

Natasha da matar Akpabio sun yi musayar baki

Takaddama kan zargin da ake yi wa Akpabio ta sake daukar sabon salo ne a lokacin da uwargidansa ta dauki matakin shari'a kan Sanata Natasha.

Misis Ekaette Akpabio ta musanta zargin cewa Akpabio ya nemi yin lalata da Natasha, tana mai cewa mijinta mutum ne mai mutunta mata da son shigarsu gwamnati.

Sai dai, Sanata Natasha ba ta dauki kalaman Misis Ekaette da wasa ba, inda ta aika mata sakon gargadi a kan 'hawainiyarki ta kiyayi ramata', da kuma 'da mijinki nake yi ba da ke ba.'

Kara karanta wannan

Ana binciken Natasha maimakon Akpabio duk da zargin shugaban majalisa da lalata

A wasikar da ta aika wa matar Akpabio ta hannun lauyanta, Victor Giwa, Sanata Natasha ta bukaci Misis Ekaette ta guji shiga cikin wannan takaddama.

'Karya take yi': Martanin Akpabio ga Natasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya musanta zargin cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.

Mai ba Akpabio shawara kan harkokin yada labarai, Kenny Okulogbo, ya bayyana cewa duk zargin da Natasha ke yi ba su da tushe ko makama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com