"Ɗan Takara 1 Tal gare Mu," Sanatan APC Ya Hango Wanda Zai Ci Gaba da Mulkin Najeriya a 2027

"Ɗan Takara 1 Tal gare Mu," Sanatan APC Ya Hango Wanda Zai Ci Gaba da Mulkin Najeriya a 2027

  • Sanata Orji Kalu ya ce ɗan takara ɗaya tal jam'iyyar APC gare ta a zaɓen shugaban kasa na 2027 kuma shi ne Mai girma Bola Ahmed Tinubu
  • Tsohon gwamnan jihar Abia ya ce duk da inyamurai na son su mulki ƙasar nan amma ya zama dole a bari Tinubu ya karisa shekaru takwas
  • Kalu ya rarrashi ƴan Najeriya kan su kara hakuri da Shugaban kasa Tinubu domin babu yadda za a yi mai rauni ya warke a rana guda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana da ɗan takara guda ɗaya tilo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sanata Kalu ya ce APC ba ta ɗa wani ɗan takara da ya wuce Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu a zaɓen 2027 domin ya zama dole ya yi shekara takwas a kan mulki.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya taso El Rufai a gaba, ya fadi asarar da ya jawo ga APC

Sanata Orji Kalu.
Sanata Kalu ya yi ikirarin cewa babu wanda zai ja da Tinubu a APC Hoto: Orji Uzor Kalu
Source: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Abia ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da tashar Channels TV cikin shirinsu na siyasa a yau a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce duk da su na son a samu shugaban ƙasa daga yankin Inyamurai, ba a kan zaɓen 2027 wannan batu yake ba, domin kuwa dole ne Shugaba Tinubu ya yi tazarce.

Inyamurai na son karɓar mulkin Najeriya

Sanata Kalu ya ce Kudu maso Gabas na fatan wata rana ya karɓi mulki, amma dole ne yankin ya fito ɗan takarar da za a iya amincewa da shi a faɗin Najeriya.

"Ba zan yi dogon bayani kan batun samar da shugaban ƙasa daga cikin Inyamurai ba, amma har yanzu ina da ra’ayin cewa akwai bukatar hakan.
"Ya kamata Inyamurai su nemo wanda kowanne bangare na Najeriya zai yi na'am da shi. Babu wata ƙabila guda ɗaya da za ta iya samar da shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

"Ba yarbawa kaɗai ne suka zaɓi Tinubu ya zama shugaban ƙasa ba, ‘yan Najeriya ne gaba ɗaya suka zaɓe shi," in ji shi.

Tinubu: Ɗan takara 1 APC gare ta a 2027

Da aka tambaye shi a wane lokaci ne yake ganin ya dace inyamurai su shugabanci Najeriya, Kalu ya ce dole a bar Tinubu ya yi shekaru takwas, domin ana ganin alamun ci gaba.

"A jam’iyyarmu, APC, muna da ɗan takara guda ɗaya yanzu, kuma shi ne shugaba Tinubu. Dole ne ya yi shekaru takwas. Yana gyaran tattalin arzikin ƙasa kuma abubuwa na kara ingantuwa," in ji shi.

Sanata Kalu ya ci gaba da cewa tuni shugaba Tinubu ya samu cikakken goyon bayan APC na neman wa'adi na biyu a 2027, rahoton Leadership.

Ya ƙara da cewa ba zai yiwu a warke lokaci guda ba, amma APC na da cikakken tabbacin cewa Tinubu zai zarce zango na biyu don ci gaba da ayyukan da ya fara.

2027: Tinubu na da ƙalubale a Arewa

A wani labarin, kun ji cewa Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa da alamu ƴan Arewa sun fusata da yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulkinsa.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

Tsohon gwamnan Kaduna ya ce tallar Tinubu za ta yi wahala a zaɓen 2027 saboda yadda yake nuna wariya da naɗa yaransa a muƙaman gwamnati.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262