Ana Zarginsa da Neman Matar Aure, Shugaban Majalisa Ya Nemi Gwamna Ya Koma APC

Ana Zarginsa da Neman Matar Aure, Shugaban Majalisa Ya Nemi Gwamna Ya Koma APC

  • Shugaban Majalisar dattawa, Godwill Akpabio ya ce zai shirya gangami na musamman idan gwamnan Abia, Alex Otti ya dawo APC
  • Sanata Akpabio ya bayyana haka a wurin taron ƙarin shekarar Sanata Abaribe na APC, wanda gwamnatin Abia ta shirya masa ranar Asabar
  • Tsohon ministan harkokin Neja Deltan ta kuma yabawa salon siyasar Gwamna Otti da kuma dimbin ci gaban da yake kawo wa al'ummarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya yabawa Gwamna Alex Otti da sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Abaribe bisa ƙoƙarin da suke yi.

Sanata Akpabio ya jinjinawa manyan mutanen biyu a wurin bikin cika shekara 70 a duniya na Sanata Abaribe, wanda gwamnatin Abia ta shirya.

Akpabio da Gwamna Alex Otti.
Shugaban Majalisar dattawa ya fara zawarcin Gwamna Alex Otti zuwa APC Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Punch ta ce da yake jawabi a taron ranar Asabar, Sanata Akpabio ya yabawa Gwamna Otti tare da fatan wata rana zai tattara ya koma jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ana binciken Natasha maimakon Akpabio duk da zargin shugaban majalisa da lalata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Akpabio ya jinjinawa Otti bisa kyakkyawar siyasarsa, yana mai cewa hakan ya kara masa karbuwa a zukatan mutanen Abia.

Shugaban majalisa ya fara zawarcin gwamna

Ya kuma bayyana cewa idan Otti ya amince da shiga jam’iyyar APC, to zai shirya masa babban biki domin nuna girmamawa ta musamman.

“Otti yana da kyakkyawar zuciya kuma yana son jin dadin jama’arsa, yadda kake girmama Abaribe duk da bambancin jam’iyya yana nuna cewa ka goge a siyasa.
“Ka riga ka sace zukatan mutanen Abia ta Kudu ta hanyar girmama Sanata Abaribe. Idan lokaci ya yi na neman karin wa’adi, za ka ga cewa wannan matakin da ka dauka yana da fa’ida.”
“Na ga ayyukan alherin da kake yi a jihar, amma ba zan yaba da su a fili ba, domin har yanzu kana LP. Idan ka shigo APC, za ka ji cikakken yabon da zan maka.”

-Godswill Akpabio

Akpabio ya jinjinawa Sanata Abaribe

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware kudin ciyarwa a Ramadan, ta fadi abin da za ta kashe

Bugu da kari, Shugaban Majalisar Dattawa ya yabawa Sanata Abaribe bisa kishin kasa da jarumtarsa, musamman kan yadda ya tsaya wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, domin samun beli.

“Sanata Abaribe mutum ne mai sadaukarwa, cikakken dan kabilar Igbo. A lokacin da ka tsaya wa Nnamdi Kanu a kotu, mutane da dama sun yi mamaki.
"Amma ka ce kana da cikakken amanna da shi, har ma ka amince da zama a kurkuku idan har ya gudu," in ji shi.
Godwill Akpabio.
Shugaban Majalisar dattawa ya yi wa Gwamnan Abia tayin shiga APC Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

An buƙaci matasa su yi koyi da Abaribe

A karshe, Akpabio ya bayyana Abaribe a matsayin abin koyi ga matasan Najeriya, yana mai cewa rayuwarsa cike take da darussa na gaskiya, kishin kasa da biyayya ga al’umma.

“Mun taru a nan ne domin girmama mutumin da ya cancanci hakan. Abaribe jigo ne a cikin al’ummar Igbo da Najeriya baki daya.”

Atiku ya nemi a binciki Akpabio

A wani rahoton, kun ji cewa Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan zarge-zargen cin zarafi, tsoratarwa, da rashin adalci da ake yi a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gudanar da bincike mai zurfi kan zargin Akpabio da neman lalata da Sanata Natasha Hadiza Akpoti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262