Gwamna Ya shiga Matsala, Majalisar Dokoki Ta ba Shi Sa'o'i 48 Ya Bayyana a gabanta
- Majalisar dokokin jihar Ribas karkashin jagorancin Martin Amaewhule ta ba Simi Fubara kwanaki biyu ya sake gabatar da kafin kudin 2025
- Wannan wa'adi na zuwa ne bayan kotun kolin Najeriya ta tabbatar da tsagin Amaewhule na Majalisar dokokin a matsayin halastacce
- A zaman da suka yi yau Litinin a Fatakwal, ƴan Majalisar sun buƙaci mai girma gwamna ya sake gabatar da kasafin kuɗin domin amincewa da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Rikicin siyasar jihar Ribas ya ɗauki sabon salo yayin da Majalisar dokoki ta ba Gwamna Sim Fubara wa'adin sa'o'i 48 ya bayyana a gabanta.
Majalisar Dokokin Ribas ta ba Gwamna Fubara kwanaki biyu kacal ya gurfana a gabanta domin ya sake gabatar da kasafin kudin 2025.

Asali: UGC
Channels tv ta tattaro cewa ƴan Majalisar sun cimma wannan matsaya ne a zaman da suka yi yau Litinin, 3 ga watan Maris, 2025 a Fatakwal, babban birnin Ribas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna ya rattaɓa hannu a kasafin 2025
A ranar 2 ga watan Fabrairu, Fubara ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin 2025 wanɗa zai laƙume Naira tiriliyan 1.1, bayan gabatar da shi ga tsagin Majalisa wanda Victor Oko-Jumbo ke jagoranta.
Sai dai, bayan watanni da gabatar da kasafin, Kotun Koli ta yanke hukunci da ke tabbatar da Martin Amaewhule da ‘yan majalisar da yake jagoranta a matsayin halattattun 'yan Majalisar dokokin Ribas
Wannan hukunci da kotu ta yanke a makon jiya, ya kawo ƙarshen rikicin shugabanci da ya dabaibaye majalisar tsawon lokaci.
Kotun koli ta yi hukunci kan rikicin Ribas
Bayan wannan hukunci, Kotun Koli ta kuma umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya riƙe kuɗin jihar Ribas har sai an bi umarnin kotu yadda ya kamata.
Bugu da ƙari, kotun ta soke zaben kananan hukumomin jihar da aka gudanar a shekarar da ta gabata, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
A martanin da ya mayar bayan hukuncin kotun ƙoli, Gwamna Fubara ya sanar da shirinsa na gudanar da sabon zaben kananan hukumomi a jihar Ribas.
A cikin jawabinsa ga ‘yan jihar, Fubara ya buƙaci ciyamomin da kotu ta tsige su miƙa mulki ga shugabannin sashen gudanarwa na kananan hukumomi.
Gwamnan ya sha alwashim cewa zai aiwatar da hukuncin kotun mai daraja ta ɗaya, wacce ta tsige ciyamomin saboda an saɓa doka wajen shirya zaɓen.

Asali: Twitter
Majalisa ta dawo da batun kasafin 2025
Amma a zaman farko da suka gudanar bayan wannan hukunci, Majalisar dokokin Ribas karkashin Amaewhule ta bukaci Gwamna Fubara da ya sake gabatar da kasafin kuɗin 2025.
Ƴan Majalisar sun nemi Fubara ya bayyana gabansu kuma ya gabatar da kasafin kudin domin su tantance shi kafin amincewa da shi ya zama doka.
Kotun koli ta tsige ciyamomi 23
A wani labarin, kun ji cewa Kotun Kolin Najeriya ta sauke dukkan shugabannin ƙananan hukumomin jihar Ribas daga kam muƙamansu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa an tafka kura-kurai a zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar ranar 5 ga watan Oktoba a jihar Ribas.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng