Shugaban Majalisa Ya Yi Magana kan Zargin Ya Nemi Yin 'Lalata' da Sanata Natasha

Shugaban Majalisa Ya Yi Magana kan Zargin Ya Nemi Yin 'Lalata' da Sanata Natasha

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karyata zargin cin zarafin da Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta yi masa
  • Sanata Akpoti-Uduaghan ta yi ikirari a wata hira da aka yi da ita cewa Akpabio ya nemi yin lalata da ita a matsayin sharadin goyon bayan kudirinta
  • Sai dai mai magana da yawun Sanata Akpabio, Kenny Okulogbo, ya musanta zargin, yana mai cewa karya ce kuma ba ta da tushe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya mayar da martani kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta yi masa.

Godswill Akpabio ya musanta zargin da abokiyar aikinsa ta yi masa na cewa ya nemi lalata da ita a matsayin sharadin goyon bayan ƙudirorinta a Majalisa.

Kara karanta wannan

'Ba haka ba ne': Matar Akpabio ta yi barazana ga Natasha, ta fallasa tsohuwar alakarsu

Natasha da Akpabio.
Shugaban Majalisar Dattawa ya musanta neman lalata da Sanata Natasha Hoto: NGRSenate
Asali: Twitter

Sanata Akpoti-Uduaghan, ‘yar jam’iyyar PDP, ta yi wannan zargi ne yayin wata hira da Arise TV a safiyar ranar Juma’a, 28 ga Fabrairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta jefi Akpabio da zargi

Ta bayyana cewa Akpabio ya nemi yin lalata da ita, wanda hakan ya zama tushen matsalolinta da take fuskanta a Majalisar Dattawa.

Sanata Natasha ta yi wannan ikirari ne bayan Majalisar dattawa ta nemi ta gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa domin kare kanta kan zargin rashin ɗa'a.

Tun farko dai rikici ya shiga tsakanin shugaban Majalisar dattawa da Sanata Natasha daga jihar Kogi ne kan tsarin zama a zauren Majalisar dattawa.

Akpabio da Natasha sun yi cacar baki mai zafi kafin daga bisani shugaban majalisar dattawan ya bayar da umarnin a fitar da ita daga zauren majalisar.

Ya ɗauki wannan matakin ne saboda ta kalubalanci umarnin da ya ba ta na sauya mata wurin zama.

"Zargin Sanata Natasha ƙarya ne" - Akpabio

Kara karanta wannan

Natasha: Yadda tsohuwar shugabar NDDC ta mari Akpabio kan zargin lalata a 2020

Da yake mayar da martani a wata hira da jaridar Punch, mai ba Shugaban Majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai, Kenny Okulogbo, ya ya ƙaryata zaegin.

Mista Oƙulogbo ya bayyana cewa duk zargin da Natasha ta yi cewa Akpabio ya neme ta da lalata ba gaskiya ba ne.

Akpabio.
Shugaban majalisar dattawa ya ce Sanata Natasha ta masa karya, bai taɓa nemanta ba Hoto: @NGRSenate
Asali: Facebook

Akpabio zai maida martani da kansa

Ya ce nan ba da jimawa ba Godswill Akpabio zai maida martani kan zargin da kansa, sannan za mu fitar da sanarwa mai ƙunshe da cikakken bayani.

“Duk abin da Sanata Natasha ta fada karyace kawai. Ta fusata ne saboda an cire ta daga shugabancin Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da harkokin albarkatun ƙasa.
"Shugaban Majalisar dattawan da kansa zai mayar da martani, za mu fitar da sanarwa a hukumance nan gaba.”

Zargin lalata: Sanatar Abuja ta tsoma baki

A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ireti Kingibe da ke wakiltar Abuja a Majalisar Dattawa ta tsoma baki kan rigimar da ta shiga tsakanin Natsaha Akpoti da Godswill Akpabio.

Kara karanta wannan

'Akpabio ya neme ni da lalata': Sanata Natasha ta tona asirin shugaban majalisa

Sanata Kingibe ta bayyana cewa ta yi matuƙar mamaki game da zargin Natasha ta yi cewa shugaban majalisa ya nemi lalata da ita, inda ta ce babu wacce Akpabio ya fi fifita wa kamar ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262