Tsohon Makusancin Peter Obi Ya Hango Rugujewar LP, Ya Fadi Makomarsa a 2027
- Tsohon dan takarar gwamna a jihar Anambra, Valentine Ozigbo ya yi tone-tone a kan halin da tsohuwar jam'iyyarsa ta LP ta ke ciki
- Mista Ozigbo, wanda ya taya Peter Obi fafutukar neman zama shugaban Najeriya a zaben 2023, ya fice daga jam'iyyar bisa wasu dalilai
- Ya kara da cewa a yanzu haka, tattauna wa tsakanin Peter Obi da wasu jam'iyyu sun yi nisa, a kokarin samar da hadaka gabanin zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Wani makusancin tsohon dan takarar shugaban kasa a LP, Valentine Ozigbo ya ce zai iya tabbatar da cewa Peter Obi ba zai sake neman kujerar a inuwar jam'iyyar ba.
Ozigbo, wanda kusa ne a cikin ƙungiyar Obidient Movement, ya fice daga PDP a 2022 sannan ya shiga LP domin tallafa wa burin Obi na zama shugaban kasar nan.

Asali: Twitter
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa Ozigbo ya ce ya ce abubuwa da dama suna afkuwa a jam'iyyar, wanda ya sa har ya iya bugun kirji a kan cewa ba zai sake neman takarar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin abubuwan da ya ce suna afkuwa akwai maganganu da ake yi na yin hadaka da wasu jam'iyyun adawa gabanin babban zabe mai karato wa.
Kusa a LP hango rushewar jam'iyyar LP
Channels TV ta ruwaito cewa Valentine Ozigbo ya bayyana cewa akwai alamu masu nuna cewa jam’iyyar LP ba za ta kai ruwa rana ba, musamman idan aka duba yadda siyasa ke tafiya a yanzu.
Ya ce:
“Ba na ganin wata makoma ga LP a nan gaba. Na yarda da wannan matsayi, amince wa da hakan ya sa na samu sanyi a rai na.
“Peter Obi wanda mu ke magana a kansa ma ya bar ANPP zuwa APGA, daga nan zuwa PDP sannan zuwa LP.
Zan iya kusan tabbatar da cewa idan yana son sake yin takara, ba zai kasance a ƙarƙashin LP ba. Zan iya kusan tabbatar da hakan.”
Makusancin Peter Obi ya fadi makomar LP
Daya daga cikin makusantan na Peter Obi ya bayyana cewa duk da ba shi ne mai magana da yawun tsohon ɗan takarar ba, amma yana da fahimtar abubuwa da ke faruwa.

Asali: Twitter
Mista Ozigbo ya ce:
“Ba ni ne mai magana da yawunsa ba. Wataƙila na yi kuskure, amma shaida ne ga tattaunawa da dama da suka shafi haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyu."
Yayin da yake tunawa da zamansa a PDP, Ozigbo ya ce zaɓen fidda gwani a lokacin shugabancin Uche Secondus ya kasance mai adalci da gaskiya.
Sai dai ya ce sauyin shugabanci a jam’iyyar ya canja yadda abubuwa ke tafiya, lamarin da ya shafi nasararta a siyasa.
Yadda jam'iyyar LP ta fada cikin rikici
A baya, kun ji cewa tsohon dan takarar gwamna a jihar Anambra, Valentine Ozigbo ya fice daga LP zuwa APC, yana mai cewa ya yanke shawarar hakan ne saboda kishinsa ga makomar jiharsa.
A cikin takardar murabus ɗinsa, tsohon shugaban kamfanin Transnational Corporation of Nigeria ya ce ya sanar da Peter Obi game da ficewa daga LP a matsayin girmamawa ga jagorancinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng