Siyasar Najeriya: Ana Fatan Peter Obi Ya Sauya Sheka zuwa APC

Siyasar Najeriya: Ana Fatan Peter Obi Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Bayan ficewarsa daga jam’iyyar LP zuwa APC, Valentine Ozigbo ya ce yana fatan Peter Obi zai bi sahunsa wajen sauya sheka a siyasa
  • Valentine Ozigbo ya bayyana cewa ya tattauna da Obi kafin yanke shawarar ficewa daga LP, amma bai bukace shi da ya shiga APC ba
  • Ozigbo ya ce rikicin cikin gida da ke addabar LP ne ya sa ya bar jam’iyyar, yana mai cewa abin ya fi na jam'iyyun PDP da APC hadari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar gwamna a Anambra, Valentine Ozigbo, ya bayyana cewa yana fatan tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, zai shiga jam’iyyar APC a gaba.

Valentine Ozigbo ya bayyana haka ne bayan ficewa daga LP zuwa jam'iyyar APC a kwanaki kadan da suka gabata.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

Peter Obi
Tsohon jigon LP na fatan Obi ya koma APC. Hoto: Mr. Peter Obi
Asali: Twitter

Ozigbo ya yi bayani ne a wata hira da aka yi da shi a wani shiri na tashar Channels TV a ranar Alhamis, 27 ga Fabrairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Ozigbo, wanda ya fice daga LP zuwa APC kwanan nan, ya ce rikicin cikin gida da ke addabar LP ne ya sa ya sauya sheka.

Ozigbo ya fice daga LP saboda rikicin jam'iyya

A cewar Ozigbo, ya fice daga jam’iyyar LP ne saboda yadda rikicin cikin gida ya cabe, ya bayyana cewa jam’iyyar ta fi PDP da APC rikici.

Ya ce tun kafin ya yanke shawarar ficewa, ya tattauna da duk mutanen da ya dace ya tuntuba, ciki har da Peter Obi.

Ozigbo ya ce lokacin da suka yi taro a Anambra domin zaben shugabanni na jam’iyyar LP, an gudanar da shi ne cikin rashin gaskiya, lamarin da ya sa ya daina jin dadin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan kusoshin APC sun kaurace wa taron jam'iyya, Tinubu ya dora wa Ganduje aiki

Ana fatan Peter Obi zai shiga APC

A yayin da aka tambaye shi ko ya bukaci Obi da ya sauya sheka zuwa APC, Ozigbo ya ce bai bukace shi da hakan ba, amma yana fatan wata rana zai yanke wannan shawara.

A cewarsa:

“Na gaya masa wasu abubuwa, amma ba batun shiga APC ba. Amma zan yi maraba da shi idan har wata rana ya yanke shawarar hakan.”

Ya kara da cewa bayan ya sanar da Obi cewa ba zai iya tsayawa takara a karkashin LP ba, washegari sai ya koma APC domin ya yi bankwana da jam'iyyar.

Ozigbo
Tsohon dan LP mai fatan Obi ya koma APC. Hoto: Valentine Ozigbo
Asali: UGC

Ozigbo: Rikicin LP ya fi na PDP da APC

Ozigbo ya ce rikicin da ke addabar LP ya fi wanda ke cikin PDP da APC hadari, inda ya bayyana cewa hakan ne ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.

Ya ce ba zai iya ci gaba da kasancewa a jam’iyyar da ba ta da shugabanci na gari ba, don haka ya ga cewa abu mafi dacewa shi ne ya bar ta.

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

Ozigbo ya bayyana cewa yana da kyakkyawan fata ga APC, kuma yana sa ran samun hadin kai domin ci gaba da tafiya da manufofin jam’iyyar.

Mawakin Kwankwasiyya ya koma APC

A wani rahoton, kun ji cewa mawakin Kwankwasiyya, Abubakar Sani Dan Hausa ya fita daga NNPP zuwa APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya karbi Abubakar Sani Dan Hausa zuwa APC a birnin tarayya Abuja.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng