"2027 Ta Allah ce," Kwamishinan Uba Sani Ya Dankarawa El Rufai Kashedi
- Jami'i a gwamnatin Kaduna ya gargadi tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i a kan ya guji yi wa Uba Sani katsalandan a mulki
- Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarauta na Jihar Kaduna, Alhaji Sadiq Mamman Lagos ne ya yi jan kunnen
- Ya kara da cewa gwamnatin yanzu ta yi gyara kura-kuran da El-Rufa'i ya tafka a bangarori daban-daban na tafiyar da jihar Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta na Jihar Kaduna, Alhaji Sadiq Mamman Lagos, ya caccaki tsohon gwamna Nasir El-Rufai.
Kwamishinan ya tunatar da Nasir El-Rufai cewa ba shi da ikon yanke hukunci kan abin da zai faru a shekarar 2027, domin kawai Allah ne ke da ikon yin hakan.

Asali: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito kwamishinan na Allah wadai da kalaman da El-Rufai ya yi kan Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa irin wadannan kalamai ba su dace ba, kuma bai kamata a kyale su ba, sannan sam bai dace a ji tsohon gwamnan yana irin maganganun ba.
Kwamishinan Uba Sani ya gargadi Nasir El-Rufai
The Nation ta wallafa cewa Alhaji Sadiq Mamman Lagos ya yi gargadi ga tsohon gwamna El-Rufai da ya kauce wa harkokin siyasar Kaduna.
Ya bayyana cewa Allah ne kawai zai yanke hukunci kan wanda zai ci zabe a shekarar 2027, ba mutum ba, saboda haka El-Rufai ya fuskanci gabansa.
Kwamishinan ya yi wannan bayani ne a wata hira da manema labarai, yayin da kansiloli 255 na Kaduna suka bayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu da Uba Sani domin yin wa’adi na biyu.
Ya ce:
“Dole ne mu fayyace gaskiya ta hanyar tunatar da kowa cewa Gwamna Uba Sani ba ya tsoma baki a harkokin mulki tun lokacin da aka kafa wannan gwamnati. Bai taba shiga harkokin gwamnatin da ta gabata ba.”
'Gwamna Uba Sani yana aiki a Kaduna' – Kwamishina
Kwamishinan ya kara da cewa Gwamna Uba Sani ya samu nasarar gyara kuskuren manufofin tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai da suka cutar da al’umma.
Ya ce:
“Gwamna Uba Sani ya zarce tsammanin kowa, har da 'yan adawa, wadanda suka fahimci cewa shi ne shugaba da ake bukata a wannan lokaci domin hada kan al’umma da dawo da martabar jihar. Ya shafi dukkan bangarorin gwamnati domin tabbatar da nasara.”

Asali: Facebook
Kwamishinan ya kara da cewa gwamnatin Uba Sani ta mayar da kadarorin da aka kwace ko kuma aka rushe wa mamallakansu.
Haka kuma, gwamnatin ta rage kudin makaranta da gwamnatin da ta gabata ta kara.
Baya ga haka, Mamman Legas ya kuma ce an dawo da sarautar gargajiya ga manyan sarakunan da aka tube daga kujerunsu.
El-Rufa'i ya caccaki Uba Sani
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya zargi gwamnatin jihar Kaduna, a karkashin Uba Sani da mayar da batun tsaro kamar wasa.
Ya ce gwamnan da hadin kan mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu sun siyasantar da lamarin tsaro, wanda hakan ke kara ba 'yan ta'adda damar warwasa wa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng