'Ya Ci Burin Kawar da Kiristocin Kaduna': Hadimin Jonathan Ya Zargi El Rufai
- Reno Omokri ya yi zargin cewa Nasir El-Rufai na yada ƙarya kan matakan tsaron da gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka a jihar Kaduna
- Omokri ya ce gwamnatin Tinubu ta kashe shugabannin ‘yan bindiga fiye da 14, lamarin da ya kawo zaman lafiya a yankin Arewacin Najeriyaa
- Ya kuma zargi El-Rufai da kokarin kawar da al'ummar Kiristoci daga Kudancin Kaduna, amma shirin nasa ya ci tura, abin da ya sa shi takaici
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mai taimakawa shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Reno Omokri, ya yi kaca kaca da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai.
Reno Omokri ya yi ikirarin cewa Nasir El-Rufai na yada ƙarya kan matakan tsaron da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke ɗauka a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan
A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

Asali: Facebook
Reno Omokri ya yi kaca kaca da El-Rufai
'Dan siyasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno Omokri ya ce El-Rufai na cikin damuwa ne saboda gazawarsa wajen yin tasiri kan magajinsa, Sanata Uba Sani, da arkokin mulkin Kaduna.
A cewar Omokri:
"A tsawon shekara takwas da El-Rufai ya yi yana mulkin Kaduna, ba a kama ko kashe wani shugaban ‘yan bindiga ba, balle a hukunta shi."
'Yan ta'addar da aka kashe a mulkin Tinubu
Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya kara da cewa, a karkashin gwamnatin Tinubu, fiye da shugabannin ‘yan bindiga 14 da suka addabi mutane aka kashe.
"Ciki har da Kachalla Ali Kawaje, Kachalla Halilu Sububu, Kachalla Damina, Kachalla Dangote, da Kachalla Jafaru."
"Sauran 'yan bindigar da Omokri ya lissafa sun sun hada da Kachalla Barume, Kachalla Shehu, Tsoho, Kachalla Yellow Mai Buhu, Yellow Sirajo da Kachalla Dan Muhammadu."

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
"Akwai kuma Kachalla Makasko, Yellow Hassan, Boderi, Kachalla Dan Ba Birki, da Auta Dan Mai Jan Kai."
- Reno Omokri.
Omokri ya ce sakamakon wannan nasara, zaman lafiya ya dawo Kaduna da makwabtanta.
'An daina daukar hoto da 'yan bindiga' - Omokri
Faston ya ce yanzu an daina ganin hotunan manyan mutane suna ganawa da shugabannin ‘yan bindiga dauke da makamai, kamar yadda aka saba gani a zamanin El-Rufai.
Ya ce an daina biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga, maimakon haka kuwa, ana kashe su, ko a kama su, tare da gurfanar da su a gaban kotu, sannan a yanke musu hukunci.
Omokri ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu ta samu nasarori masu yawa a yaki da ‘yan bindiga, kuma kokarin da take yi ya wuce abin da aka gani a gwamnatocin baya.
'El-Rufai ya so kawo karshen Kiritoci' - Omokri
Reno Omokri ya yi ikirarin cewa tsohon gwamnan na Kaduna na jin haushin cewa hakarsa ba ta cimma ruwa ba na son kawar da Kiristoci daga Kudancin Kaduna.
Jigon na APC ya ce:
"Gaskiyar magana ita ce, Nasir El-Rufai shugaba ne da ya gaza, wanda ya jagoranci kisan kiyashin Kiristoci a Kudancin Kaduna.
"Yanzu yana takaici ne saboda shirin da ya yi na kawar da Kiristanci a Kaduna ya ci tura sakamakon ingantaccen aiki da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ke yi.
"Ba abin mamaki ba ne cewa dukkan mambobi 34 na majalisar dokokin jihar Kaduna sun zargi Malam Nasir El-Rufai da almundahana, safarar kuɗi da wasu manyan laifuka."
Daga karshe, Omokri ya bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da ikirarin El-Rufai, yana mai cewa tsohon gwamnan na kokarin bata sunan wasu ne saboda takaicinsa.
'Tinubu bai da kabilanci' - Omokri ga El-Rufai
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri ya yi tir da ikirarin cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu yana da kabilanci.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya jaddada sukar da Farfesa Farooq Kperogi ya yi game da nade-naden mukamai a gwamnatin Tinubu, abin da ya jawo Omokri yin martani.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng