"Karya Kake Yi," Ƴan Majalisa 36 Sun Yi Wa Kakaki Bore, Sun Tabbatar da Tsige Shi
- Tsohon kakakin Majalisar dokokin jihar Legas, Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya gamu da tangarɗa a ƙoƙarinsa na komawa kan kujerarsa
- Ƴan majalisa kimanin 36 sun yi fatali da ikirarin da ya yi na komawa kan shugabanci, sun jaddada cewa Mojisola Meranda ce kakakin Majalisa
- Sun bayyana cewa tsawon shekaru 10 suna hakuri da salon mulkinsa na danniya, amma a yanzu tura ta kai bango, sun tsige shi daga muƙamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Mafi yawan ‘yan Majalisar Dokokin Jihar Lagos sun nuna ɓacin ransu da komawar Mudashiru Obasa kan matsayin kakakin Majalisa a zaman yau Alhamis.
Ƴan majalisar kimanin su 36 sun jaddada cewa har yanzu Hon. Mojisola Meranda ce kakakin Majalisar dokokin jihar Legas saboda sun riga sun tsige Obasa.

Asali: Facebook
Rikicin Majalisar Legas ya tsananta
Obasa, wanda aka tsige daga kujerarsa a ranar 13 ga Janairu, ya kutsa kai cikin majalisa a ranar Alhamis tare da jami’an tsaro, abin da ya jawo cece-kuce, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ce Meranda na fuskantar matsin lamba domin ta mika mukaminta, musamman bayan rahotannin da ke nuna cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bai gamsu da sauke Obasa ba.
Bayanai sun nuna cewa an janye jami’an tsaron Meranda sannan aka mayar da na Obasa, wanda hakan ya kara tayar da kura kan kokarin dawo da shi matsayin Kakakin Majalisa karo na shida.
Yadda tsohon kakaki ya shiga Majalisa
Wata majiya ta bayyana cewa Obasa ya kutsa zauren majalisa da ƙarfin tsiya tare da wasu ƙalilan daga cikin mambobin majalisar.
Daga nan ne kuma ya jagoranci zaman majalisa, yana mai ikirarin cewa ya dawo kan kujerarsa, kamar yadda The Nation ta kawo.
Sai dai wasu daga cikin ‘yan majalisar waɗanda kuma sune masu rinjaye sun yi fatali da ikirarin tsigaggen kakaki, Mudashiru Obasa.

Asali: Twitter
Ƴan Majalisa 36 sun yi fatali da Obasa
Ƴan majalisar dokokin Legas kimanin su 36 sun nanata cewa haka kurum Obasa ba shi da hurumin mayar da kansa kan kujerar shugabanci.
Shugaban kwamitin majalisa kan karkokin tsaro da yaɗa labarai, Steven Ogundipe, ya bayyana cewa sun kuduri aniyar tabbatar da cewa matakin tsige Obasa na nan daram.
“Ba al’ummar mazabarsa suka zabe shi a matsayin Kakakin Majalisa ba. Mun shafe shekaru goma muna jure irin salon shugabancinsa na mulkin danniya.
"Amma yanzu mun yanke shawarar cewa ya ishe mu, kuma ba za mu ja da baya ba,” in ji Ogundipe.
A halin yanzu dai, rikicin na ci gaba da daukar sabon salo yayin da bangarorin biyu ke kokarin tabbatar da muradunsu.
Obasa ya dura zauren Majalisar Dokokin Legas
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ya mamaye harabar majalisar dokokin tare da tulin jami'an tsaro.
Wata majiya daga bangaren tsohon kakakin, ta tabbatar da cewa yanzu haka sun shiga ofishin, a lokacin da dambarwar majalisar ke ci gaba da ruruwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng