APC Ta Fadi Abin da zai Mayar da Tinubu Kujerarsa bayan Zaben 2027

APC Ta Fadi Abin da zai Mayar da Tinubu Kujerarsa bayan Zaben 2027

  • Jam'iyyar APC ta hade wuri guda wajen bayyana gamsuwa da yadda shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yake tafiyar da Najeriya
  • Yayin babban taron jam'iyyar da ya gudana a ranar Laraba a Abuja, APC ta nuna amincewarta don Tinubu ya sake neman takara
  • Ta bayyana cewa ayyukan da shugaban ya bijiro da su a kasar ya na haifar da da mai idan, domin jama'a sun fara gani a kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - 'Yan kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC na kasa (NEC) sun kada kuri’ar goyon baya ga shugaba, Bola Ahmed Tinubu , a daidai lokacin da ake ta ihun “babu gurbi a fadar Aso Rock.”

Wannan goyon baya ya biyo bayan rera wakar da bazarka muke rawa da ta karade dakin taron a daidai lokacin da Bola Tinubu ya isa wurin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan saukar farashin abinci, ya yi alkawarin karin sauki

Tinubu
APC na son Tinubu ya zarce Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar This Day ta ruwaito cewa Tinubu, wanda ya yi farin cikin tarbar da aka yi masa a yayin da taron, bai dakatar da wakar ba, sai dai murmushi da gyada kai da ya rika yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC ta goyi bayan Bola Tinubu

Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ne ya gabatar da kudurin kada kuri’ar goyon baya ga Tinubu, inda Sanata Adams Oshiomhole, ya mara masa baya.

Kuri’ar goyon bayan Tinubu ta zama babban abin da ya fi daukar hankali a taron, inda membobin jam’iyyar suka nuna jin dadinsu da yadda gwamnatinsa ke tafiya.

Sun bayyana amincewa da kudirorinsa, da a ganinsu yake kara farfado da tattalin arziki, da kuma inganta rayuwar 'yan Najeriya, wanda ya sa suka amince a sake neman kujerarsa.

Tinubu ya ji dadin yabon APC

Da yake gaskata 'yan jam'iyyarsa, Tinubu ya ce kasar nan na kan hanyar farfado da tattalin arzikinta, ya ambaci faduwar farashin kayayyakin abinci a matsayin babbar alama.

Kara karanta wannan

Bayan kusoshin APC sun kaurace wa taron jam'iyya, Tinubu ya dora wa Ganduje aiki

A babban taron da aka gudanar bayan shekaru biyu, Bola Tinubu ya kara jaddada aniyar ci gaba da kokarin kyautata rayuwar ‘yan Najeriya domin su ji saukin rayuwa.

Tinubu
Tinubu ya ce da gaske 'yan Najeriya suna samun saukin tsadar rayuwa Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ya ce:

“Gwamnoni, kun rungumi sauye-sauye, kuma ina godiya ga shugabannin jam’iyyarmu. Ina kuma godiya ga ‘yan majalisar tarayya bisa gaggauta nazari a kan kasafin kudi.
“Za mu iya gina jam’iyya bisa dandali na cigaba domin samar da kyakkyawar rayuwa ga ‘yan Najeriya.”

Da ya ke alkawarin ci gaba da aiki tukuru tare da sauran bangarorin gwamnati domin cimma muradun al’umma, Tinubu ya yaba da gwamnonin APC bisa jajircewarsu.

Tinubu ya yabi manufofin gwamnatin APC

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nanata cewa ana samun saukin rashin tsaro da tsadar kayan abinci, kamar yadda aka yi wa jama'a alkawari.

Ya ce:

“Ina farin ciki da saukar farashin kayayyakin abinci, musamman a gabanin watan Ramadan. Duk da yadda duniya ke fuskantar kalubale, muna ganin ci gaba a Najeriya. Muna samun dawowar zaman lafiya a hankali. Muna ganin sauye-sauye. Ina godiya, gwamnoninmu."

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC

"Na ji dadin yabonku," Tinubu ga APC

Shugaban kasa ya ce kuri’ar goyon bayan da kwamitin NEC ya kada a kansa wata alama ce ta bukatar karin aiki, inda ya yi alkawarin ba zai ba wa jam’iyya da ‘yan kasa kunya ba.

Ya ce:

“Na ji dadin kuri’ar goyon bayan da kuka kada a kaina, kuma na karba. Wannan kuri’a kalubale ce na kara tashi tsaye. Za mu dage sosai wajen tabbatar da wadatar abinci, jari da ci gaba.

Tinubu ya nemi Ganduje ya ceto APC

A baya, kun samu labarin cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci shugaban APC, Abdullahi Umar Ganduje da ya matsa lamba wajen tabbatar da an hade kan 'ya'yan jam'iyya.

Shugaban ya ba da umarnin ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke samun matsalolin cikin gida, inda wasu kusoshin APC, kamar tsohon gwamna, Nasir El-Rufa'i ke ganin ba a kyauta wa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel