Bayan Kusoshin APC Sun Kaurace wa Taron Jam'iyya, Tinubu Ya Dora wa Ganduje Aiki

Bayan Kusoshin APC Sun Kaurace wa Taron Jam'iyya, Tinubu Ya Dora wa Ganduje Aiki

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci Abdullahi Ganduje da ya kara kokari wajen sasanta ‘ya’yan jam’iyyar da suka samu sabani
  • Ya ba da umarnin ne a taron jam'iyyar da ya gudana a babban birnin tarayya a Abuja, inda wasu 'yan APC suka kauracewa
  • Sai dai Shugaban APC na kasa, Ganduje ya tabbatar da cewa tuni aka fara daukar matakan tattaunawa da masu korafi da jam'iyyar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabancin jam’iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje da su kara kokari wajen sulhunta ‘ya’yanta.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin jiga-jigan APC da suka ba da gudunmawa a zaben 2023, kamar Nasir El-Rufa'i ke takun saka da jam'iyyar.

Kara karanta wannan

APC ta fadi abin da zai mayar da Tinubu kujerarsa bayan zaben 2027

Ganduje
APC ya ba Ganduje umarnin sasanta 'yan APC Hoto: Aminu Dan Mallam
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta wallafa cewa, yayin da yake jawabi a taron NEC na 13 na jam’iyyar, Tinubu ya roki wadanda ke da korafi da su kwantar da hankalinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu yana farin ciki da aikin Ganduje

Jaridar This Day ta ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana gamsuwa da yadda Abdullahi Umar Ganduje ke tafiyar da al’amuran APC, domin ana samun ci gaba.

Ya kara da cewa:

"NWC na yin aiki mai kyau, kuma ina farin ciki da su. A kowace jiha, mu kafa kwamitin sulhu domin tuntubar shugabannin da ke da korafi. Ina rokon su da su kwantar da hankalinsu.”

A yayin babban taron, Shugaban kasa ya samu cikakken goyon bayan 'yan kwamitin zartarwa, inda suka jaddada goyon baya ga salon mulkinsa a Najeriya da sake neman takara.

Ganduje ya bayyana shirin sasanci a APC

A jawabinsa yayin bude taro, Ganduje ya tabbatar wa manyan shugabannin jam’iyyar cewa shugabancinsa ya fara babban shirin sulhunta ‘ya’yan jam’iyyar da ke da sabani.

Kara karanta wannan

An yanke makomar Ganduje, APC ta bayyana yankin da ta maida shugabancin jam'iyya

Ganduje
Shugaban APC ya ce an fara shirin sasanta masu korafi a jam'iyyar Hoto: Aminu Dan Mallam
Asali: Facebook

Ya ce:

"Ta hanyar tattaunawa, mun fara shawarwari a manyan matakai tsakanin shugabannin jam’iyya da sauran masu ruwa da tsaki domin warware sabanin da ke tsakanin membobin APC."

Ya ce wannan kokari yana haifar da sakamakon da ake bukata a jam’iyyar, yayin da ake kokarin tabbatar da ci gaba da hadin kai a APC.

Babu wasu jiga-jigan APC a taron NEC

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyya mai mulki ta APC, ta gudanar da babban taronta na kwamitin zartarwa da aka dade ana dako, amma ba a ga wasu daga cikin jiga-jiganta a taron ba.

Daga cikin wadanda ba su samu damar halartar taron ba, akwai tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, da tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi.

Sauran wadanda suka kauracewa babban taron sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr. Kayode Fayemi.

Kara karanta wannan

A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC

Sai dai APC ta bayyana cewa an aika goron gayyata ga shugabannin domin su halarci taron, wanda ke nufin ba nuna wariya ba, kuma babu laifinta a rashin zuwansu. taron.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.