Shirin Babban Taron APC Ya Gama Kankama, Jagororin Jam'iyya Sun Hallara Abuja
- 'Ya 'yan jam'iyya mai mulki ta APC sun fara hallara a sakatariyarsu da ke Abuja domin gudanar da taron APC da aka dade ana dako
- An tsaurara tsaro a titunan dake kusa da Wuse 2, Abuja da ma makwabtansu, inda ake dakon isowar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Daga cikin wadanda suka isa sakatariyar akwai tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari da kuma Hon. Benjamin Kalu
- Wannan taron zai dauki hankali matuka, ganin yadda aka dade ana dakon faruwarsa domin tattauna manyan matsalolin APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - An ƙara matakan tsaro a titin Blantyre da sauran tituna da ke makwabta da Wuse 2, Abuja a safiyar Laraba domin gudanar da babban taron jam'iyyar APC a karon farko a cikin shekaru biyu.

Kara karanta wannan
Tsohon shugaba Buhari, El-Rufa'i da sauran jagororin APC sun ki halartar taron APC
Wannan na zuwa ne yayin da jiga-jigan jam’iyyar APC ke fara isowa babban sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa domin halartar taron kwamitin zartarwarta, yayin da ake dakon wasu kusoshi a tafiyar.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ana sa ran Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da mataimakinsa, Kashim Shettima za su hallara a sakatariyar don halartar taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma ana dakon Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da takwaransa na Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas da wasu manyan APC kafin fara zaman.
Jiga-jigan APC sun sauka a Abuja
Daga cikin waɗanda suka iso har ya zuwa yanzu akwai Mataimakin shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.

Asali: Facebook
Haka nan akwai 'yan kwamitin zartarwar APC, shugabannin jam’iyya na jihohi, da tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari.
Tsohon gwamnan Jihar Kebbi kuma Ministan Tsare-tsaren Ƙasa da Kasafin Kuɗi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, shima yana daga cikin waɗanda suka halarta.
An tsaurara tsaro a taron jam'iyyar APC
An takaita zirga-zirgar ababen hawa da na mutane a wurin taron, inda kaɗan daga cikin ‘yan jarida aka ba dama domin daukar rahotannin abubuwan dake wakana.
Taron NEC na wannan karo yana da matuƙar muhimmanci ga jam’iyyar APC, domin ana sa ran tattaunawa kan manyan batutuwa da suka shafi APC.
Za a sauke Ganduje a taron APC?
Duk da cewa akwai wasu daga cikin 'yan APC dake ganin zaman Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugabansu ya saba doka, amma an musanta zargin cewa za a raba shi da kujerar.
Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Sanata Ajibola Basiru, wanda ya musanta zargin, ya kara da cewa ba zabe za a yi a taron NEC ba, saboda haka Ganduje yana kan kujerarsa.
APC za ta gudanar da taronta yau
A wani labarin, mun wallafa cewa a yau 26 ga watan Fabaraitu ne APC ke gudanar da taronta na kwamitin zartaswa na kasa (NEC) na farko tun bayan wanda aka gudanar a watan Satumbar 2023.
A wannan karon, ana sa ran jam'iyyar ta shirya gabatar da wannan taron domin tattauna muhimman batutuwa da ke shafar ci gaban jam'iyyar da harkokin siyasa a fadin Najeriya.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Ganduje, shi ne zai jagoranci taron NEC a wannan lokacin, duk da cewa akwai 'yan jam'iyya da ke adawa da cigaban zaman da yake a kujerarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng