"APC na Shirin Tafka Kuskure," Kwamanda Ya Hango Matsala kan Shugaba da Minista

"APC na Shirin Tafka Kuskure," Kwamanda Ya Hango Matsala kan Shugaba da Minista

  • Jigo a jam'iyyar APC, reshen Kano, Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda ya gargadi jam'iyyar a kan rasa karamin ministan gidaje, Abdullahi Ata
  • Dan Bilki Kwamanda na wannan batu ne a matsayin martani ga Abdullahi Abbas, bayan dambarwar da ta balle tsakaninsa da ministan tarayya
  • Ya ce matukar APC ta nade hannayenta har Ata ya fice, APC za ta gamu da gagarumar matsala, musamman a kakar zabe mai zuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Jigo a jam'iyyar APC reshen jihar Kano, Alhaji Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda, ya tofa albarkacin bakinsa a kan rikicin dake kokarin gigita jam'iyyar.

An samu musayar yawu tsakanin shugaban APC a jihar, Abdullahi Abbas, da karamin ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Abdullahi Ata kan shugabancin APC a Kano.

Kara karanta wannan

IBB: 'Dalilan kitsa harin rashin imani da ya kashe tsohon shugaban kasa, Murtala'

Kwamanda
Jagora a APC ya ba jam'iyyar shawara Hoto: AbdulMajeed Almustapha Kwamanda/Abdullahi Abbas
Asali: Facebook

A cikin hira da ya yi da Daily Trust, Dan Bilki Kwamanda ya ba da shawara ga jam'iyyar da kada ta watsar da barazanar Ata na barin APC hadi da sauka daga mukaminsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwara APC ta rasa Abbas da Ata,” in ji Danbilki.

AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya ce, zai fi dacewa a rasa mutane 100 daga tsagin shugaban APC na jihar Abdullahi Abbas fiye da a bar Ata ya fice daga cikinta.

Ya nanata cewa siyasa na bukatar mutum na mutane, wanda jama'a suka aminta ba shi, ba kamar Abdullahi Abbas ba.

Kwamanda ya gargadi shugaban APC

Dan Bilki ya shawarci Abdullahi Abbas, tare da gargadin cewa idan shugabannin jam'iyyar suka yanke shawarar tsawaita wa'adinsa, za a fuskanci babbar barazana a kakar zabe mai zuwa.

Kwamanda
Danbilki ya ba jam'iyyar APC shawara Hoto: AbdulMajeed Almustapha Kwamanda
Asali: Facebook

Ya ce:

“Muna da goyon bayan wanzuwar APC a matsayin jam'iyyar siyasa a Najeriya, kuma kowanne dan siyasa mai tunani mai kyau a Kano ya san cewa Abdullahi Abbas kamar annoba ne a APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisa 3

“Idan APC na son ta dawo da darajarta da ta rasa, Abdullahi ya tafi, kuma barazanar da ministan jihar ya yi na barin jam'iyyar ya kamata a dauke shi da muhimmanci, zai fi dacewa a rasa mutane 100 kamar Abdullahi Abbas fiye da rasa mutum guda kamar Yusuf Ata wanda ke da cikakken tarihi a cikin siyasa.”

Kwamanda ya yi wa shugaban APC shagube

Daga cikin jiga-jigan APC a Kano, AbdulMajid Dan Bilki Kwamanda ya yi mamakin kalaman shugaban jam'iyyarsa a jihar, Abdullahi Abbas, na cewa Ata ba na su bane.

Ya bayyana cewa ta yaya gwamnati za ta nada mutumin da ba dan jam'iyya a babban mukami irin na minista, bayan akwai sauran 'yan APC a kasa.

Shugaban APC ya yi martani ga Ata

A baya, kun samu labarin cewa shugaban APC na Kano, Abbdullahi Abbas ya caccaki karamin Ministan gidaje da raya karkara, Abdullahi Ata bayan barazanar cewa zai iya ficewa daga APC.

Kara karanta wannan

"Ba a shugaban APC zan dawwama ba," Abdullahi Abbas ya fadi kujerar da ya ke nema a kano

Ya ce dama Ata ya yi wa APC zagon kasa a zaben da ya gudana a 2023, wanda ya sa jam'iyyar ta zo na uku a karamar hukumarsa ta Fagge, har ma ya yi mamakin yadda ya zama Minista.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.