Bayan Kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje Sun Kira Taron Kusoshin APC a Abuja

Bayan Kalaman El Rufai, Tinubu, Shettima, Ganduje Sun Kira Taron Kusoshin APC a Abuja

  • Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci taron majalisar mashawartan APC a Abuja, karon farko tun bayan hawansa mulki a Mayun 2023
  • Shugabanni daga yankunan kasar sun halarta, ciki har da gwamnoni, ministoci, tsofaffin gwamnonin APC, da shugabannin majalisa
  • Wannan na zuwa ne cikin sa'o'i 24 da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce zai fice daga APC idan jam'iyyar ba ta saita kanta ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana jagorantar taron majalisar mashawartan jam’iyyar APC a fadar gwamnati da ke Abuja.

Wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da irin wannan taro tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kusoshin jam'iyyar APC sun shiga taro a Abuja bisa jagorancin Shugaba Tinubu
Shugaba Tinubu na jagorantar taron kusoshin jam'iyyar APC a fadar Aso Rock. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Tinubu na jagorantar taron kusoshin APC

Taron yana gudana ne a dakin taron fadar shugaban kasa (SHCC) da ke Abuja, kuma ya samu halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar, inji rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Shari'ar Yahaya Bello: Jami'an EFCC dauke da makamai sun mamaye kotu a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce taron ne zai bada damar gudanar da taron majalisar zartarwa na jam’iyyar NEC da aka shirya yi a hedikwatar APC da ke Wuse 2, Abuja, a ranar Laraba.

Daga cikin manyan shugabannin da suka halarta akwai mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, kakakin majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.

Ganduje ya samu rakiyar mambobi tara na kwamitin ayyuka na kasa (NWC), ciki har da mataimakan shugaban jam’iyya na Arewa da Kudu, sakataren jam’iyya na kasa, mai ba da shawara kan harkokin shari’a, ma’aji, sakataren tsare-tsare, shugabar mata, shugabar matasa, da shugabar nakasassu.

Abubuwan da ake sa ran za a tattauna a taron

Gwamnonin APC, karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma, wanda ke shugabantar kungiyar gwamnonin 'progressive' (PGF) sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Barau ya rikita Kano da kyautar motoci da babura, ya yi alkawari ga matasa da malamai

Wasu daga cikin batutuwan da ake tattaunawa sun hada da shirin gudanar da babban taron da ba zabe ba, wanda ya dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Tinubu ya jagoranci taron majalisar mashawartan APC a karon farko tun bayan hawa mulki.
Tinubu, Shettima, Ganduje, Akpbio sun halarci taron majalisar mashawartan APC na kasa. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Ana kuma sa ran cewa za a duba batun kafa kwamitocin dindindin na jam’iyyar, gabatar da shirin cibiyar TPI, da aiwatar da rajistar mambobi ta intanet.

A yayin taron, ana sa ran za a tattauna rahoton da mai ba da shawara kan harkokin shari’a ya gabatar kan shari’un da ke gaban kotuna da suka shafi jam’iyyar.

Kusoshin APC da suka halarcin taron

Gwamnonin APC da suka halarta sun hada da Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Dapo Abiodun (Ogun), Babagana Zulum (Borno), Uba Sani (Kaduna), Ahmad Aliyu (Sokoto), Umar Bago (Neja) da Rev. Fr. Hyacinth Alia (Benue).

Shugabannin yankin kudu maso kudu na jam’iyyar APC, karkashin jagorancin tsohon gwamnan Bayelsa Timipre Sylva, sun halarci taron.

Daga yankin Arewa, wasu daga cikin jiga-jigan da suka halarta sun hada da Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan Nasarawa Tanko Al-Makura, Sanata Aliyu Wammako, da ministan kasafin kudi da tsare-tsare Abubakar Bagudu.

Kara karanta wannan

2027: PDP da APC sun fara cacar baki kan shigar El Rufa'i cikin 'yan adawa

Shugabannin jam’iyyar daga yankin kudu maso yamma, ciki har da Bisi Akande, Iyiola Omisore, Olusegun Osoba, sun hallarci taron.

Sanata Tahir Monguno da Sanata Lola Ashiru suma sun halarci zaman.

Tsohon kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara, tsohon gwamnan Cross River Prof. Ben Ayade, da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Sanata Anyim Pius Anyim suma sun kasance a wajen taron.

'APC ce ta yi watsi da ni' - El-Rufai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce yana jira APC ta yi taron majalisar zartarwa da na mashawarta don ganin matakin gyara da za ta dauka.

Mallam Nasir El-Rufai ya ce idan har jam'iyyar ba ta koma kan turbar da aka santa ba, zai sauya sheka yana mai cewa APC ce ta yi watsi da shi, ba shi ne ya bar ta ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.