2027: Jigon APC a Kudu Maso Kudu Ya Fadi Lokacin Hadaka da El Rufa'i

2027: Jigon APC a Kudu Maso Kudu Ya Fadi Lokacin Hadaka da El Rufa'i

  • Tsohon ɗan majalisar wakilai, Israel Sunny-Goli, ya soki kiran da Nasir El-Rufai ya yi na ƙawancen Arewa da yankin Kudu-Maso-Kudu
  • Sunny-Goli ya ce Najeriya tana hannun na gari a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu, kuma ba ta buƙatar wani ceton gaggawa
  • Sai dai duk da haka ya bayyana lokacin da za su iya yin hadakar siyasa da Nasir El-Rufa'i domin yin tafiya daya tare da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bayelsa - Wani jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon ɗan majalisar wakilai, Israel Sunny-Goli, ya mayar da martani kan kiran hadaka da tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya yi.

A makon da ya wuce Malam Nasir El-Rufai ya bukaci kafa ƙawance tsakanin yankin Arewa da Kudu Maso Kudu.

Kara karanta wannan

"Mun raba gari," El-Rufa'i ya fadi abin da ya kashe abotarsa da Uba Sani, Ribadu

Tinubu
Jigon APC ya yi martani ga El-Rufa'i kan neman hadaka da Kudu Maso Kudu. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa Sunny-Goli ya ce kiran da El-Rufai ke yi ba daidai ba ne, yana mai cewa hakan wata hanya ce ta dagula lamura.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ya yi furucin ne a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga dangin marigayi Edwin Clark, inda ya ce Najeriya na fuskantar barazana, kuma yankin Niger Delta na da rawar da zai taka.

'Najeriya na hannun na gari' – Sunny-Goli

A cewar Israel Sunny-Goli, shugaba Bola Ahmed Tinubu na aiki tukuru don magance matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da gwamnatin baya ta bari.

Tribune ta wallafa cewa Israel Sunny-Goli ya ce:

“Ba boyayyar magana ba ce cewa wannan gwamnati ta gaji tattalin arziƙi da matsalolin tsaro da suka daɗe suna addabar ƙasa, amma yanzu muna samun ci gaba.
"Sojojin Najeriya na ƙoƙarin murƙushe ‘yan ta’adda tare da dawo da zaman lafiya.”

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i ya fadi kalubalen da za a fuskanta wajen tallar Tinubu a Arewa

Sunny-Goli ya yabi Tinubu kan nadin mukamai

Sunny-Goli ya jaddada cewa yankin Kudu Maso Kudu yana da manyan mukamai a gwamnatin Tinubu, wanda hakan ke nuna cewa yankin yana da kyakkyawar alaƙa da shugaban ƙasa.

Ya lissafo wasu daga cikin manyan mukaman da mutanen yankin ke rike da su, ciki har da:

  • Nyesom Wike – Ministan Babban Birnin Tarayya
  • Sanata Godswill Akpabio – Shugaban Majalisar Dattawa
  • Dr Heineken Lokpobiri – Ministan Albarkatun Man Fetur (Mai)
  • Hon Ekperikpe Ekpo – Ministan Albarkatun Man Fetur (Iskar Gas)
  • Dr Samuel Ogbuku – Daraktan NDDC
  • Felix Omatsola Ogbe – Shugaban NCDMB
  • Festus Keyamo – Ministan Sufurin Jiragen Sama da Fasahar Sararin Samaniya
Nasir
Tsohon gwamnan Kaduna yana jawabi a wani taro. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Yaushe Kudu za ta yi hadaka da El-Rufa'i?

Sunny-Goli ya ce wataƙila a shekarar 2031 za a iya tattauna batun ƙawance, amma a halin yanzu suna goyon bayan shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi abin rashin jin dadi da APC ta yi masa da matakin da zai dauka

A ƙarshe, Sunny-Goli ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara wa gwamnatin Tinubu baya, domin ya samu damar aiwatar da shirye-shiryensa na kawo ci gaba ga ƙasa baki ɗaya.

2027: El-Rufa'i ya yi magana kan tallata Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i ya ce za a sha wahala wajen tallata Bola Tinubu a 2027.

A karkashin haka, tsohon gwamnan ya yi kira da cewa ya kamata Bola Tinubu ya sauya salon tafiyarsa tun kafin lokaci ya kure masa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel