"Akwai Sauran Rigima": Kotu Ta Yi Hukunci kan Batun Tsige Ɗan Majalisar Zamfara
- Babbar kotun tarayya mai zama a Gusau ta dakatar da shirin tsige shugaban marasa rinjaye na Majalisar dokokin Zamfara, Aliyu Ango Kagara
- Mai shari'a Salim Olasupo Ibrahim ya umarci kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa har sai kotu ta yi hukuncin ƙarshe a shari'ar da ke gabanta
- Tun farko majalisar dokokin ta tsige Hon. Kagara daga kujerarsa ta ɗan Majalisa mai wakiltar Talata Mafara ta Kudu saboda rashin halartar zama
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Jagoran ƴan adawa a Majalisar dokokin jihar Zamfara watau shugaban marasa rinjaye, Hon. Aliyu Ango Kagara ya yi nasara a ƙarar ya shigar gaban kotu.
Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Gusau a Zamfara, ta dakatar da yunƙurin da Majalisar Dokokin jihar ta yi na tsige Hon. Aliyu Ango Kagara.

Asali: Facebook
Rahoton Leadership ya tattaro cewa Hon. Aliyu Kagara na wakiltar mazaɓar Talata Mafara ta Kudu a zauren Majalisar dokokin jihar Zamfara ƙarƙashin inuwar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan Majalisa ya kai ƙara gaban kotu
Wannan mataki ya biyo bayan ƙara mai lamba FHC/GSCS/10/2025, da Hon. Kagara ya shigar gaban kotun yana ƙalubalantar shirin tsige shi.
Waɗanda ɗan Majalisar ya shigar ƙara sun haɗa da Majalisar dokokin Zamfara, kakakin Majalisa, da hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta.
Tun farko dai Majalisa ta sanar da tsige Hon. Aliyu Kagara daga kujerar dan Majalisar Talata Mafara saboda rashin halartar zama kamar yadda doka ta tanada.
Me ya sa majalisa ta tsige Hon. Aliyu?
Majalisar ta ce duk wani yunƙuri na sasantawa da kwamitocin sulhun da ta kafa suka yi bai haifar da sakamakon da ake so ba, shiyasa ta kore shi gaba ɗaya.
Ta umarci hukumar zaɓe watau INEC ta shirya zaɓen cike gurbi domin ba mutanen Talata Mafara ta Kudu damar sake zaɓen ɗan Majalisarsu.
Sai dai sakamakon rashin gamsuwa da wannan mataki, ɗan Majalisar ya garzaya gaban babbar kotun tarayya mai zama a Gusau yana ƙalubalantar tsige shi domin mutane ne suka zaɓe shi.
Kotu ta ɗauki mataki kafin gama shari'a
A hukuncin da ya yanke ranar Talata, Alkalin kotun, mai shari'a Salim Olasupo Ibrahim, ya bayar da umarnin hana INEC gudanar da zaben cike gurbin mazabar Talata Mafara.
Ya kuma umarci kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa ma'ana ɗan Majalisar ya koma kan kujerarsa har sai kotu ta gama sauraron karar kuma ta yanke hukunci.
Daga nan kuma sai alkalin ya daga sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Maris, 2025.
Majalisar dokokin jihar Zamfara dai ta jima tana fama da rikici, inda a baya ta dakatar da ƴan Majalisa tara kan dalilai daban-daban

Asali: Facebook
Ƴan Majalisa sun yi zanga-zanga a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa dakatattun ƴan Majalisar dokokin jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja.
A cewarsu, duk wata doka da ragowar ƴan Majalisa 14 suka ɗauka ciki har da amincewa da kasafin kudin 2025 ya saɓawa doka domin ba su kai biyu bisa uku ba.
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa,
Asali: Legit.ng