"Mun Raba Gari," El Rufa'i Ya Fadi Abin da Ya Kashe Abotarsa da Uba Sani, Ribadu
- Tsohon gwamna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana takaicin yadda tsofaffin abokansa ke kokarin rage tasirin siyasarsa gabanin zaben 2027
- Ya zargi gwamna Uba Sani na jihar Kaduna da mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da kitsa makarkashiya
- Sai dai yana ganin har yanzu, mutanen da yake zargi sun kasa samun nasarar dakile siyasarsa, duk da barazana ga mukarrabansa da ake yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya ce mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Gwamnan Kaduna, Uba Sani sun tashi daga abokansa.
Ya yi zargin cewa tsofaffin abokan nasa biyu na ƙulla makircin bata masa suna, wanda ke nuni da rashin jituwa da ke tsakaninsa da Gwamna Uba Sani da tsohon ubangidansa a yanzu.

Asali: Facebook
A wata hira da ya yi da Arise TV a ranar Litinin, El-Rufa’i ya ce Ribadu ne ke jagorantar wani yunkuri na raunata siyasar 'yan hamayya kafin zaɓen 2031.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufa’i: "Ribadu na son lalata siyasata"
PR Nigeria ta wallafa cewa El-Rufa’i na zargin mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ne ke jagorantar wani shiri da nufin murƙushe siyasarsa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce:
“Wannan shiri na rushe siyasar Nasir El-Rufa’i tunanin Nuhu Ribadu ne. Shi ne ya tsara shi, kuma shi ne ke aiwatar da shi.
Shi ne ke aiki tare da Uba Sani don ganin an kammala wannan shiri. Sai dai har yanzu, abin bai tafi yadda suke so ba.”
El-Rufa’i ya bayyana shirin Ribadu a kansa
El-Rufa’i ya ƙara da cewa ana amfani da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) domin matsawa tsofaffin mukarrabansa lamba don a tozarta shi.
Ya ce:
“Gaskiya abin da suke yi yanzu shi ne kiran mutane ƙanana da wasu daga cikin mukarrabaina su ce, ‘ku fallasa El-Rufa’i, matsalarku za ta ƙare.’ Wannan shi ne abin da ICPC ta zama.”
El-Rufa’i ya barranta kansa da Ribadu da Uba Sani
Tsohon gwamnan, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da nasarar Uba Sani a matsayin magajinsa, ya bayyana takaicinsa kan yadda dangantakarsu ta lalace.

Asali: Facebook
Ya ce:
“Uba Sani da Nuhu Ribadu ba abokaina ba ne. Sun kasance abokaina a baya, amma yanzu ba haka ba ne.”
Kalaman El-Rufa’i na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da samun ce-ce-ku-ce kan siyasa da zarge-zargen binciken cin hanci da rashawa da ke da alaƙa da wa’adinsa na gwamnan Kaduna.
El-Rufa’i: "Ba zan sake takara ba"
A wani labarin, mun wallafa cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa ba shi da niyyar sake tsayawa takara don jama'a su zabe shi a gangamin zaben siyasa mai zuwa.
Ya ce dama tun can shi ba dan siyasa ne mai neman takara ba, domin hatta kujerar gwamna da ya samu, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne ya tilasta masa neman mukamin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng