SDP ko PDP?: Jam'iyyar da Nasir El Rufai zai koma idan Ya Fice daga APC

SDP ko PDP?: Jam'iyyar da Nasir El Rufai zai koma idan Ya Fice daga APC

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi watsi da duk wata magana da ke cewa yana shirin komawa babbar jam’iyyar adawa ta PDP
  • El-Rufai ya bayyana cewa PDP ta kara tabarbarewa, kuma tun tuni ya yanke shawarar cewa ba zai taba komawa wannan jam’iyya ba
  • Sai dai tsohon gwamnan bai kawar da yiwuwar ficewa daga APC ba, idan jam’iyyar mai mulki ta kasa komawa kan ginshikanta na farko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai taba komawa PDP ba, yana mai cewa jam’iyyar ta rushe gaba daya.

El-Rufai ya ce ya jima da yanke shawarar cewa PDP ba jam’iyyar da zai iya komawa ba ce, domin a cewarsa, ta zama mafi muni a tarihin siyasa.

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i ya fadi kalubalen da za a fuskanta wajen tallar Tinubu a Arewa

El-Rufai ya yi magana kan yiwuwar komawa PDP gabanin 2027
El-Rufai ya bayyana dalilin da zai sa ya fice daga jam'iyyar APC da inda zai koma. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da Arise TV a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu.

El-Rufai na duba yiyuwar barin APC

Duk da haka, El-Rufai bai kawar da yiwuwar ficewa daga APC ba, yana mai cewa idan har APC ta kasa komawa kan ginshikan da aka kafa ta a kai, zai nemi wata sabuwar jam’iyya da ta dace da manufofinsa.

Tsohon gwamnan ya ce har yanzu yana cikin jam’iyyar APC mai mulki, amma jam’iyyar ce ta rabu da shi, ba wai shi ne ya rabu da ita ba.

Ya ce ba shi kadai ba ne a wannan hali, domin akwai sauran ‘yan jam’iyyar da dama da aka mayar saniyar ware daga harkokin gudanar APC.

El-Rufai ya kara da cewa abin takaici ne yadda jam’iyyar ba ta gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) tsawon shekaru biyu, wanda hakan ya sabawa irin manufofin da suka assasa APC.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi abin rashin jin dadi da APC ta yi masa da matakin da zai dauka

A cewarsa, irin wannan halin yana kara tabbatar da cewa jam’iyyar ta bar manufofin da ta fara tafiya a kansu.

Dalilin sa-in-sa tsakanin El-Rufai da shugabannin APC

El-Rufai ya yi magana kan yiwuwar ficewa daga jam'iyyar APC
El-Rufai ya ce akwai yiwuwar ya fice daga APC idan ba ta gyara tafiyarta ba. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito cewa a kwanan nan, El-Rufai ya yi kaca-kaca da shugabannin APC da gwamnatin shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa sun bar alkawuran da suka daukarwa ‘yan Najeriya.

El-Rufai ya ce tun yanzu ba ya jin kansa a cikin jam’iyyar, kuma abubuwan da ke faruwa sun sa ya rasa gane ina APC ta sa gaba.

Wannan furuci nasa ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda mutane da dama suka fara hasashen cewa zai fice daga APC.

Sai dai a yayin ganawar tasa da Arise TV, El-Rufai ya jaddada cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar, amma ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen fadin gaskiya kan abubuwan da ke faruwa.

A cewarsa, idan dai APC ta kasa komawa kan manufofin da aka gina ta a kai, zai bar jam’iyyar don ya nemi wata da ta fi dacewa da akidunsa.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa a kan sake neman takara a Najeriya

A karshen hirar, tsohon gwamnan ya ce abin da ya fi damunsa shi ne yadda wasu jiga-jigan APC suka mayar da jam’iyyar tamkar tasu su kadai, ba tare da la’akari da ra’ayoyin sauran mambobi ba.

Ga bidiyon hirar a nan kasa:

El-Rufai ya fadi wanda yake so ya karbi mulki

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya bayyana goyon bayansa ga samun dan kudu a matsayin magajin Bola Tinubu a 2027.

Tsohon gwamnan Kaduna na cikin manyan ‘yan siyasar Arewa da ke kokarin hada kai don kalubalantar gwamnatin Tinubu a zabe mai zuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com