2027: El Rufa'i Ya Fadi Kalubalen da za a Fuskanta wajen Tallar Tinubu a Arewa

2027: El Rufa'i Ya Fadi Kalubalen da za a Fuskanta wajen Tallar Tinubu a Arewa

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce akwai alamun fushi a Arewacin Najeriya kan yadda Bola Tinubu ke tafiyar da mulki
  • Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa ba wai Tinubu na nada Yarbawa ba ne gaba daya, amma kawai mutanen da yake da kusanci da su da yake ba mukami
  • El-Rufai ya ce har yanzu ba a makara ba, inda ya ce shugaba Bola Tinubu na da damar gyara lamarin domin dawo da daidaito a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa akwai matsanancin fushi a Arewacin Najeriya kan yadda shugaba Bola Tinubu ke tafiyar da mulki.

Tsohon gwamnan ya ce Bola Tinubu na ba da mafi yawan mukamai ga mutanen da suke kusa da shi daga Legas.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi abin rashin jin dadi da APC ta yi masa da matakin da zai dauka

El Rufa'i
El-Rufa'i ya bukaci Bola Tinubu ya gyara tafiyarsa. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

El-Rufai ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a Arise TV, ya ce akwai rashin daidaito a nade-naden da ake yi a gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai duk da haka, El-Rufai ya ce ba laifin kabilar Yarbawa ba ne, amma matsalar tana da nasaba da yadda Tinubu ke fifita yaran gidansa.

'Tinubu na ba yaransa mukami' – El-Rufai

El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ba yana nada Yarbawa ne gaba daya ba, sai dai kawai yana bai wa mutanen da suke kusa da shi daga Legas mukamai.

El-Rufa'i ya ce:

“Mafi yawan nade-naden da ake yi ba su shafi daukacin Yarbawa ba, sai dai kawai mutanen da suka fito daga kusa da Tinubu.”

Ya kara da cewa dole a fuskanci gaskiya a kan wannan lamari.

“Nade-naden ba su daidaita ba, wannan abu ne bayyananne. Amma ba matsalar kabilanci ba ce.

Kara karanta wannan

'Don Allah ka bar ni': Ribadu ya yi martani ga El-Rufai bayan kalamansa kan zaben 2031

"Don Allah, ka da a dauki Yarbawa a matsayin masu laifi, kamar yadda ake la'antar 'yan Arewa saboda laifin sojojin mulkin mallaka.”

'A gyara kafin lokaci ya kure' – El-Rufai

Tsohon gwamnan ya ja hankalin shugaba Tinubu da cewa har yanzu yana da damar gyara kura-kuransa, domin hakan zai taimaka wajen kwantar da fushin al'umma.

EL Rufa'i
El-Rufa'i da shugaba Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga|Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Nasir El-Rufa'i ya ce:

“Shugaba Tinubu na bukatar yin wani abu don daidaita wannan lamarin. Har yanzu bai makara ba, zai iya gyara matsalar.”

El-Rufai ya ce akwai rashin jin dadi a Arewa, kuma mutanen da ke kewaye da Tinubu ba za su iya komawa can su ce a zabi APC ko Tinubu ba.

Ya ce ya isar da sakon nan ta wasu da ke kusa da Shugaban kasa Tinubu, yana fatan za su samu kwarin gwiwar sanar da shi gaskiya.

Har yanzu ina APC Inji Nasir El-Rufa'i

Kara karanta wannan

'Ku tambaye shi, ya sani': El-Rufai ya fadi yadda Buhari ya tilasta masa neman gwamna

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya ce har yanzu yana cikin jam'iyyar APC duk da matsalolin da suka dabaibaye tafiyar jam'iyyar.

El-Rufa'i ya ce ba zai koma PDP ba amma akwai mataki na musamman da zai dauka idan ya ga lamura sun ki daidaituwa a APC a gaba kadan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng