El Rufa'i Ya Fadi Matsayarsa a kan Sake Neman Takara a Najeriya

El Rufa'i Ya Fadi Matsayarsa a kan Sake Neman Takara a Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana burin da yake da shi a siyasar Najeriya tun bayan barin mulki a 2023
  • A hira da ya yi karo na farko tun bayan ya bar ofis, El-Rufa’i ya ce tun can shi ba dan siyasa mai neman takara ba ne a kasar nan
  • Ya bayyana bangaren da ya fi kwarewa a fannin siyasa, ya kara da cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyarsa sai ya ga abin da zai turewa buzu nadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KadunaTsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana shirin da yake da shi a siyasar Najeriya tun bayan barin mulkin jiharsa a shekarar 2023.

El-Rufa’i, wanda ya danganta nasarar da ya samu a zaben da ya gabata da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa shi ba ɗan siyasa mai neman takara ba ne.

Kara karanta wannan

"Mun raba gari," El-Rufa'i ya fadi abin da ya kashe abotarsa da Uba Sani, Ribadu

Kaduna
Tsohon gwamnan Kaduna ya fadi yadda ya nemi takara a baya Hoto: Nasir El–Rufa'i
Asali: Facebook

A wata hira da ya yi da Arise News a yammacin Litinin, tsohon gwamnan ya ce kafin ya nemi takarar gwamnan Kaduna, bai taɓa neman wata kujera a siyasar Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda El-Rufa’i ya nemi kujerar gwamnan Kaduna

A hira da ya yi karo na farko tun bayan barin ofis a shekarar 2023, Nasir El-Rufa’i ya ce tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ne ya tilasta masa neman kujerar gwamna.

Ya ce;

“Ban so zama gwamna ba. Tsohon shugaba Muhammadu Buhari ne ya tilasta mani. Za ka iya tambayarsa a kowane lokaci.
Na ji tsoron neman kujerar, domin ban taɓa tsayawa takarar komai ba a gwamnati.
“Ni ma’aikaci ne. Mutane suna neman takara, amma idan sun samu aikin da ya fi ƙarfinsu, sai su ba wa mutane kamar ni don su tabbatar da cewa an yi aikin.”

El-Rufa’i: “Ba zan tsaya takara ba”

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana cewa ba zai taɓa barin siyasa ba, amma ba shi da niyyar ci gaba da neman wasu kujeru a gwamnati.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi abin rashin jin dadi da APC ta yi masa da matakin da zai dauka

Arise
El Rufa'i ba ya neman takara Hoto: @Dan_alhajj
Asali: Twitter

Ya ƙara da cewa zai ci gaba da zama a jam’iyyarsa domin tabbatar da cewa an ci gaba da kasancewa a turbar da aka gina ta.

Sai dai, yana ganin cewa idan aka bijire wa manufar jam’iyya, zai tattara kayansa ya nemi wata jam’iyyar da muradunta suka zo ɗaya da nasa domin ci gaba da hidimtawa al’umma.

El-Rufa’i bai son Tinubu ya koma mulki

A wani labarin, mun ruwaito cewa Nasir El-Rufa’i ya bayyana matsayinsa kan batun zaben 2027, ya ce yana goyon bayan samun wani ɗan Najeriya daga yankin Kudu da zai maye gurbin Bola Tinubu.

A cewarsa, gara a samu sabon shugaba daga Kudu ya maye gurbin shugaban kasar, a maimakon Bola Tinubu ya zarce kamar yadda wasu manyan APC bukatar hakan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.