Bayan Dakatar da Yan Majalisar NNPP 4, Jam'iyyar APC Ta Gamu da Matsala a Kano

Bayan Dakatar da Yan Majalisar NNPP 4, Jam'iyyar APC Ta Gamu da Matsala a Kano

  • Jim kaɗan bayan dakatar da ƴan Majalisar Tarayya 4, NNPP ta karbi dubban masu sauya sheka a ƙaramar hukumar Gwarzo a Kano
  • Ƴan APC aƙalla 1,500 daga mazaɓu daban-daban a ƙaramar hukumar Gwarzo sun bar tafiyar tsintsiya, sun koma jam'iyya mai alamar littafi
  • Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam ne ya tarbi masu sauya sheƙar a hukumance a ofishinsa da ke gidan gwamnati

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Akalla mambobi 1,500 na jam’iyyar APC a jihar Kano sun sauya sheka zuwa NNPP mai mulki.

Wannan sauya sheka na zuwa ne bayan jam'iyyar NNPP ta dakatar da ƴan Majalisar tarayya guda huɗu ciki har da Sanata Kawu Sumailla bisa zargin cin amana.

Aminu Abdulsalam.
Dandazon mambobin APC sun sauya sheka zuwa NNPP a jihar Kano Hoto: @alameen
Asali: Twitter

Wadanda suka sauya shekar sun fito ne daga gundumomi daban-daban a ƙaramar hukumar Gwarzo ta jihar Kano, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mataimakin gwamna ya tarbi masu shiga NNPP

Sun samu kyakyyawar tarba daga mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdulsalam a gidan gwamnati ranar Litinin.

A yayin taron da aka gudanar a ofishinsa, Aminu Abdulsalam ya bayyana cewa matakin da suka dauka na shiga NNPP da cewa ya zo a lokacin da ya dace.

A cewarsa, sauya sheƙarsu zai ƙara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf goyon baya wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da kyautata wa al'umma.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin gwamna, Ibrahim Shuaibu, ya fitar a ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, 2025

Aminu Abdulsalam ya tabbatar wa sababbin ƴan NNPP da cewa za su samu dama iri ɗaya da kowane ɗan jam'iyya, ba za a nuna masu banbanci ba.

"Muna farin cikin maraba da ‘yan uwammu cikin NNPP, hakan ya na kara tabbatar da yadda jama’a suka aminta da manufofin jam’iyyarmu a Kano da Najeriya baki daya," in ji shi.

Kara karanta wannan

Malam El Rufai ya bayyana wanda yake so ya karɓi mulki daga hannun Tinubu a 2027

Dalilin da ya sa suka baro jam'iyyar APC

Jagororin tawagar masu sauya shekar, Malam Abdullahi Tiga da Aliyu Sulaiman, sun bayyana cewa sun bar APC ne saboda gazawar jam’iyyar wajen cika burikan al’umma.

Sun kuma tabbatar da cikakken goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir da shugabannin jam'iyyar NNPP a Kano.

Sun kuma yaba da yadda gwamnatin NNPP ke kokarin aiwatar da ayyukan raya kasa da inganta rayuwar talakawa a Kano.

Malam Abdullahi Tiga ya kara da cewa:

"Mun dauki wannan mataki ne domin ci gaban jama’a, domin mun fahimci cewa jam’iyyar APC ta kauce daga ainihin kudurorinta na yi wa talakawa hidima."

Bayanai daga wasu daga cikin wadanda suka sauya sheka

Aliyu Sulaiman, daya daga cikin shugabannin masu sauya sheka, ya ce suna da yakinin cewa NNPP za ta ba su dama su taka rawar gani a tafiyar siyasar Kano.

Wadanda suka sauya sheka sun nuna shirin hada kai da sabbin abokan tafiyarsu a NNPP domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a nan gaba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƴan majalisa 3

Bayan kammala taron, mataimakin gwamnan ya ja hankalin sababbin ‘yan jam’iyyar da su rike gaskiya da aiki tukuru domin ci gaban Kano da NNPP.

A cewar Aminu Abdulsalam

"Muna bukatar hadin kai da amana domin dorewar tafiyar NNPP. Wannan ba sauya sheka kawai ba ne, a’a, alƙawari ne na hidima ga al’umma."
NNPP da APC.
Dubannin ƴan APC sun sauya sheka zuwa NNPP a Kano Hoto: @officialAPCNig
Asali: UGC

Bugu da kari, Shugaban Karamar Hukumar Gwarzo, Dr. Mani Tsoho, ya ba wa masu sauya shekar tabbacin cewa za a ba su damar daidai da sauran mambobi.

Jiga-jigai da magoya baya da suka halarci taron sun jaddada aniyarsu ta karfafa NNPP domin fuskantar zabukan gaba, tare da yin kira ga al'umma musamman ƴan siyasa su shigo jam’iyya mai mulki.

Rurum ya yi fatali da dakatarwar NNPP

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya ce jam'iyyar NNPP ɗin da yake ciki ba ta da alaƙa da wacce ta dakatar da shi.

Kara karanta wannan

Ganduje ya firgita NNPP, ya fadi jiga jigan jam'iyyar da za su dawo APC

Hon. Kabiru Rurum ya jaddada cewa shi da takwarorinsa ba su da wata alaƙa da ɓangaren da ya canza tambarin jam’iyyar watau tsagin Kwankwaso.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262