Rikicin NNPP: Dan Majalisa Ya Yi Martani kan Dakatarwar da Aka Yi Masa, Ya Yi Fallasa
- Kabiru Alhassan Rurum ya taɓo batun dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano
- Ɗan majalisar mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure a majalisar wakilai ya yi watsi da matakin jam'iyyar NNPP
- Kabiru Rurum ya bayyana cewa tuni ya raba gari da NNPP mai alamar littafi domin ya daɗe da ficewa daga tafiyarsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Ɗan majalisa mai wakiltar Rano, Kibiya da Bunkure, Kabiru Alhassan Rurum, ya yi magana kan dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar NNPP a Kano.
Ɗan majalisar ya yi watsi da dakatarwar, yana mai bayyana hakan a matsayin matakin da babu tushe balle makama kuma raina hukuncin kotu ne.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ɗan majalisar ya bayyana hakan ne lokacin da yake maida martani kan dakatarwar da aka yi masa daga NNPP.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan majalisa ya nesanta kansa daga NNPP a Kano
Kabiru Alhassan Rurum ya jaddada cewa shi da takwarorinsa ba su da wata alaƙa da ɓangaren da ya canza tambarin jam’iyyar, yana mai cewa suna cikin wani ɓangare daban na NNPP.
A kwanakin baya ne dai Kabiru Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini suka nesanta kansu daga tafiyar Kwankwasiyya, inda suka bayyana cewa su na ɓangaren NNPP mai tambarin kayan marmari.
“Duniya ta sani cewa tun da suka canza tambarin jam’iyyar, ba mu tare da su. Mu muna cikin NNPP mai tambarin kayan marmari, yayin da su ke da tambarin littafi. Muna da hukuncin kotu wanda ya yi watsi da iƙirarinsu."
- Kabiru Alhassan Rurum
Ya zargi shugabancin NNPP na Kano da bijirewa hukuncin kotu, yana mai cewa:
"Abin da suka yi raina kotu ne. Ba su da halaccin shugabancin jam’iyyar. Bayan nasarar da muka samu, sun kai mu wata kotu a Abia, har ma a wannan makon mun sake zuwa kotu. Su na yaudarar ƴan Najeriya."

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin gwamnan PDP ya haɗa kai da gwamnatin Tinubu, ya fara yi wa APC aiki
Kabiru Rurum ya yi fallasa a NNPP
Rurum ya danganta dakatarwar da aka yi masa da ɗaurin auren ƴar Sanata Kawu Sumaila, wanda ya ce manyan mutane daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarta.
Ya yi zargin cewa shugabancin jam’iyyar, ciki har da jagoran tana ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso, sun samu goron gayyata amma suka ƙi halartar ɗaurin auren.
"Babban abin da ke damun su, wanda bai kamata ma a siyasantar da shi ba, shi ne ɗaurin auren ƴar Sanata Kawu Sumaila.
Manyan mutane sun halarta, ciki har da Kwankwaso an gayyace shi, amma suka ki halarta."
Kabiru Alhassan Rurum ya yi watsi da dakatarwar da aka masa, yana mai cewa ɓangarensu na cin gashin kansa ne.
"Kowa a wannan kasa ya san cewa muna tafiya ne daban da su. Su ne kawai suka dakatar da kansu, domin ba mu tare da su."
- Kabiru Alhassan Rurum
'Yan majalisar NNPP za su sauya sheƙa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan mambobin NNPP da za su sauya sheƙa.
Ganduje ya bayyana cewa sun shirya tarbar manyan jami'ai, sanatoci da ƴan majalisar wakilai da za su sauya sheƙa daga NNPP zuwa jam'iyyar APC.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng