Ganduje: Rawar da Bola Tinubu Ya Taka wajen Karya Farashin Abinci

Ganduje: Rawar da Bola Tinubu Ya Taka wajen Karya Farashin Abinci

  • Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya yabawa sauye-sauyen tattalin arzikin Bola Tinubu, yana mai cewa suna haifar da ci gaba
  • Ganduje ya bayyana haka ne a yayin wani shirin tallafi da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya yi a jihar Kano
  • Shugaban jam'iyyar ya bukaci al’ummar jihar Kano su goyi bayan gwamnatin Tinubu domin tabbatar da ci gaba a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa na haifar da ci gaba.

Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a wani shirin tallafi da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya shirya a Kano, inda aka raba motoci da babura ga jagororin APC.

Kara karanta wannan

El Rufa'i: APC ta hango barazana a 2027, ta bukaci Tinubu ya dauki mataki

Ganduje
Ganduje ya bayyana kokarin da Tinubu ke wajen kawo sauki Najeriya. Hoto: Salihu Tanko Yakasai|Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar the Nation ta ruwaito cewa Ganduje ya yabawa Tinubu bisa kokarinsa na farfado da tattalin arzikin Najeriya da kuma samar da ci gaba a fannoni daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganduje ya yabawa sauye-sauyen Tinubu

A yayin taron, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa tsarin mulkin Tinubu yana tafiya daidai kuma yana haifar da ci gaba a kasar.

Ganduje ya ce:

"A karkashin jagorancin shugaba Tinubu, mun shaida yadda tattalin arzikin Najeriya ke samun ingantaccen ci gaba.
"Sauye-sauyen da ake aiwatarwa sun haifar da karin ayyukan yi, inganta abubuwan more rayuwa da bunkasar wasu sassa na tattalin arziki."

Rage farashin kaya da farfado da Naira

Abdullahi Ganduje ya kara da cewa tsarin Tinubu ya taimaka wajen rage farashin kayan abinci, rage farashin fetur da kuma karfin da Naira ta samu a kasuwar hada-hadar kudi.

Jaridar Peoples Gazette ta wallafa cewa shugaban APC ya ce:

Kara karanta wannan

Barau ya rikita Kano da kyautar motoci da babura, ya yi alkawari ga matasa da malamai

"Sauye-sauyen sun kawo raguwar farashin kayayyakin abinci, farashin fetur ya ragu, sannan Naira ta fara karfi.
"Wannan na cikin sakamakon kyawawan manufofin gwamnatin Tinubu."

Tinubu bai manta Kano ba inji Ganduje

Ganduje ya bayyana cewa Shugaba Tinubu na mutunta Kano sosai, wanda ya sa ya ba da manyan mukamai ga ‘yan jihar.

Daga cikin mukaman da aka bai wa ‘yan Kano akwai Shugaban APC na kasa, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ministoci biyu, da sauran manyan mukamai.

Ganduje ya yabawa Barau Jibrin

Shugaban APC ya jinjinawa Barau Jibrin bisa kokarinsa na kafa Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yamma tare da godewa Tinubu bisa amincewa da ita.

Ganduje ya bukaci al’ummar Kano da su mara wa gwamnatin Tinubu baya domin ci gaba da aiwatar da tsare-tsaren da za su amfani Najeriya baki daya.

Sanata Barau ya bukaci hadin kai a APC

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ministan Tinubu ya yi bayani kan barazanar ficewa daga APC

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya bayyana cewa jagorancin Ganduje ya kara karfin APC.

Barau
Mataimakin shugaban majalisar dattawa yayin wani jawabi. Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Twitter

Sanata Barau ya ce:

"A karkashin Ganduje, jam’iyyarmu ta samu karfi sosai. Mun samu nasarori da dama kuma muna fatan ci gaba da bunkasa jam’iyyar a karkashin jagorancin sa."

Barau Jibrin ya bukaci mambobin jam’iyyar APC da su hada kai domin mara wa Shugaba Tinubu baya wajen ci gaba da gina kasa.

Sanata Barau ya raba motoci da babura

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Barau Jibrin ya raba motoci da babura ga shugabannin jam'iyyar APC a jihar Kano.

Bayan raba motoci da baburan, Sanata Barau Jibrin ya ce wannan somin tabi ne domin shirye shiryen tallafi masu yawa za su biyo baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng