"Ba a Shugaban APC zan Dawwama ba," Abdullahi Abbas Ya Fadi Kujerar da Ya ke Nema a Kano

"Ba a Shugaban APC zan Dawwama ba," Abdullahi Abbas Ya Fadi Kujerar da Ya ke Nema a Kano

  • Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya bayyana cewa ba so ya ke ya yi ta zama a matsayin shugaban jam'iyya ba
  • Wannan na zuwa a lokacin da karamin ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata ya zarge shi da kokarin komawa kujerarsa
  • A martaninsa, Abdullahi Abbas ya ce kujerar da ya ke harara tafi ƙarfin shugabancin APC a kakar zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jiar KanoHar yanzu martanin shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas na ci gaba da daukar hankula, musamman bayan da ya furta cewa kujerar gwamna ya ke harara.

Wannan na daga cikin jerin martanin da ya yi ga karamin ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Abdullahi Ata na barazanar ficewa daga jam'iyya.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa

Abbas
Abdullahi Abbas ya fara neman kujerar gwamna Horo: Hon. Abdullahi Abbas
Asali: Facebook

A hirar da ya yi da BBC Hausa, Abdullahi Abbas ya ce kalaman Ata na zuwa ne a lokacin da ba a gama komai a kan shirya zaben shugabancin jam'iyya a jihar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa, shugaban APC na ganin Ata ya yi riga malam masallaci wajen bayyana fargabar Abdullahi Abbas zai koma kujerar a karo na hudu.

APC: "Ata ba ɗan siyasa ba ne"

Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas ya yi zargin cewa karamin Ministan gidaje a gwamnatinsu ba wani fitaccen ɗan siyasa ba ne.

Abbas
Abdullahi Abbas ya yi martani ga Ata Hoto: Hon. Abdullahi Abbas
Asali: Facebook

Abdullahi Abbas, ya bayyana Ata da;"

Ai ba ɗan siyasa ba ne, ɗan siyasa ne na ƙaramar hukuma kawai. Mu muka saka shi a shugaban majalisa, shi ma ya kasa, aka cire shi. Saboda haka ba ɗan siyasa ba ne gogagge."
"A Kano gaba ɗaya, a ƙaramar hukumarsa mu ka yi na uku a Fagge, kuma ba mu sani ba aka ba shi Minista. Kuma har shugaban kasa mun gaya wa, ba ɗan jam'iyya ba ne."

Kara karanta wannan

Kano: APC ta rikirkice, shugaban jam'iyya ya ragargaji ministan Tinubu

Martanin jama'a ga shugaban jam'iyyar APC

Wasu daga cikin masu amfani da shafin Facebook sun bayyana mamakin yadda Abdullahi Abbas zai fito ƙarara neman kujerar gwamna a Kano.

Wata Maryam Ibrahim Naala ta ce;

"Kano ai sai Abba In Sha Allah.

Fariki Photos Dandago ya ce;

Allah ya tsare Kano da yan sumunka.

Muslim Mg Bature;

Subhanallah. To ku rubuta ku ajiye ba gwamnan kano ba, ko shugaban jama"iyyar ma ba zai sake komawa ba.

Abdullahi Dahiru ya ce;

"Shugaban masu tada hatsaniya yache komai zai faru zai zama gwamna Allah kaji damu alheri.

Manyan APC sun samu sabani a Kano

A wani labarin, mun wallafa cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Abbas ya caccaki ƙaramin ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Abdullahi Ata bayan ya soke shi.

A wani taro da ya gabata a ƙaramar hukumar Fagge, Ata ya bayyana cewa su masu tarbiyya ne, kuma irin kalaman da Abdullahi Abbas ya yi a baya ne ya sa APC ta rasa gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ministan Tinubu ya yi bayani kan barazanar ficewa daga APC

A martanin shugaban na APC ya ce dama tun can ministan ba ɗan APC ba ne, hasali ma ya yi wa jam'iyyar zagon ƙasa a zaben 2023, inda suka yi rashin nasara ya na kallo.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel