Siyasar Kano: Ministan Tinubu Ya Yi Bayani kan Barazanar Ficewa daga APC
- Ministan gidaje da raya Birane, Abdullahi Ata, ya musanta rahotannin da ke cewa yana barazanar ficewa daga jam'iyyar APC
- Abdullahi Ata ya ce an sauya kalamansa daga ainihin abin da ya faɗa yayin taron APC a Kano, inda ya yi kira ga hadin kai
- Ata ya jaddada goyon bayansa ga shugaba Bola Tinubu, Sanata Barau Jibril, da Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Ministan Gidaje Abdullahi Ata ya karyata rahotannin da ke cewa yana barazanar ficewa a APC idan har aka bar shugaban APC a Kano, Abdullahi Abbas, a kan mukaminsa.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Ata ya bayyana cewa an fitar da kalamansa daga asalin ma’anar su, tare da yada labarin da ka iya haddasa rabuwar kai a cikin jam’iyyar APC.

Source: Original
PM News ta ruwaito cewa sanarwar, wacce mai taimaka wa Ministan a harkokin yada labarai, Seyi Olorunsola, ya sa wa hannu, ta bukaci ‘yan jarida su guji yada rahotanni marasa inganci.
Minista ya musanta barazanar ficewa a APC
Abdullahi Ata ya bayyana cewa wasu ‘yan jarida sun cire kalamansa daga mahallinsu domin kawo rarrabuwar kai a cikin jam'iyyar APC.
A cewarsa, yayin taron APC a karamar hukumar Fagge, da kuma ganawarsa da tsofaffin ‘yan majalisar dokokin jihar Kano, ya jaddada bukatar hadin kai don karfafa APC a zaben 2027.
Bukatar hadin kai a cikin jam'iyyar APC
Ministan ya ce dole ne APC ta kasance tsintsiya madaurinki daya domin samun ci gaba da nasarar shugaba Bola Tinubu, Sanata Barau Jibril da sauran jiga-jigan jam’iyyar a Kano.
Ya kuma yi gargadin cewa shugabannin da ke amfani da kalaman da ke rarraba kan jama’a, ko kuma bata sunan addini da al’adu, na iya haifar da matsala ga jam’iyyar a nan gaba.

Kara karanta wannan
"Ba a shugaban APC zan dawwama ba," Abdullahi Abbas ya fadi kujerar da ya ke nema a kano
A karkashin haka ya ce ya yi maganganu ne kan hadin kan jam'iyya ba wai neman raba kan mambobin jam'iyyar ba.

Source: UGC
Minista ya jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar APC
Ata ya tabbatar da cewa yana nan daram a APC, kuma yana tare da shugabancin jam’iyyar a matakin kasa da na jihar Kano.
Ya kuma bukaci ‘yan jarida da su rika bin ka’idojin aikin jarida, su guji yada rahotannin da ke haifar da rudani a cikin al’umma.
A karshe, ya bukaci mambobin APC su kasance masu biyayya, tare da yin aiki tukuru domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a zaben 2027, har ma da dawo da mulkin Kano hannun APC.
APC ta yi magana kan makomar siyasar El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar PDP da APC sun fara cacar baki kan makomar siyasar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.
Haduwar Nasir El-Rufa'i da jiga jigan 'yan jam'iyyun adawa daban daban ya jawo APC martani tare da zargin cewa yana haka ne saboda rasa mukamin minista.

Kara karanta wannan
'A gyara': Minista ya yi barazanar ficewa daga APC kan shugabancin jam'iyyar a Kano
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng
