2027: PDP da APC Sun Fara Cacar Baki kan Shigar El Rufa'i cikin 'Yan Adawa
- Jam’iyyar APC ta zargi tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da tayar da rigima saboda gazawarsa wajen samun mukamin minista
- A ‘yan makonnin nan, El-Rufai yana ganawa da manyan ‘yan siyasan Arewa da kuma jiga-jigan adawa, ciki har da Atiku Abubakar
- PDP ta bayyana cewa tana shirye don yin aiki tare da El-Rufai da sauran ‘yan siyasa domin ceto Najeriya daga mulkin APC a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jam’iyyun APC da PDP sun kaure da cacar baki kan matakin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na hada kai da manyan ‘yan siyasar Arewa da 'yan adawa.
Ana ganin El-Rufai na kokarin hada kan manyan ‘yan siyasa domin kalubalantar takarar tazarcen shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027.

Asali: Facebook
Punch ta wallafa cewa matakin ya jawo ce-ce-ku-ce a APC, inda ta zarge shi da kokarin tayar da rikici a siyasar Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito cewa a makonnin nan, El-Rufai ya gana da Atiku Abubakar, tsohon dan takarar shugaban kasa a PDP, tare da sauran jiga-jigan 'yan adawa, wanda hakan ya kara jawo rudani.
APC ta zargi El-Rufai da tayar da rigima
Sakataren APC na kasa, Ajibola Basiru, ya caccaki El-Rufai yana mai cewa yana amfani da kabilanci a siyasarsa saboda gazawarsa wajen samun mukamin minista.
Bayan El-Rufai ya kammala wa’adin gwamnatinsa a Kaduna, an nada shi minista, amma Majalisar Dattawa ta hana shi samun mukamin bisa dalilan tsaro.
Tun daga wannan lokacin, dangantakarsa da shugaba Bola Tinubu ta fara yin tsami musamman a baya-bayan nan.
El-Rufai na hada kai da ‘yan adawa
A kwanakin nan, El-Rufai ya shiga jerin taruka da jiga-jigan adawa, ciki har da Atiku Abubakar, wanda a baya ba su zama a inuwar siyasa daya.

Kara karanta wannan
2027: El-Rufai ya fadi yankin da ya dace ya hada kai da Arewa domin ceto Najeriya
Bayan ganawar su, El-Rufai ya raka Atiku zuwa ziyarar ta’aziyya ga iyalan Edwin Clark, jigo a yankin Niger Delta.
A yayin ziyarar, El-Rufai ya yaba da rawar da Atiku ya taka wajen tsara manufofin tattalin arziki a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo.

Asali: Facebook
PDP ta ce a shirye take ta hada kai da El-Rufai
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana maraba da kowa da kowa da ke da burin ceto Najeriya daga APC.
Mai magana da yawun PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya ce El-Rufai yanzu ya fahimci cewa PDP ce jam’iyyar da ke mutunta doka da oda.
Debo Ologunagba ya ce:
"A jam’iyyarmu, ana rajaistar membobi a matakin mazabu da kananan hukumomi. Kofar PDP a bude take ga kowa."
Tun bayan da El-Rufai ya fara furta kalaman caccakar APC, jam’iyyar PDP ke ganin cewa hakan wata alama ce ta sabuwar hadaka da wasu jiga-jigai da za su iya sauya sheka a zaben 2027.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar
'Yan adawa sun fara shirin 2027
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyun adawa na cigaba da shirye shiryen karawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Jiga jigan 'yan adawa sun bayyana cewa ba za su yi wasa ko sakaci ba kamar yadda suka yi wajen rashin hada kai a zaben 2023.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng