2027: Jigon PDP Ya Jijjiga Tebur, Ya Fadi Abin da Ke Shirin Faruwa da APC a Arewa

2027: Jigon PDP Ya Jijjiga Tebur, Ya Fadi Abin da Ke Shirin Faruwa da APC a Arewa

  • PDP ta ce babu ɗan Arewa mai hankali da zai goyi bayan APC a 2027, tana zargin gwamnatin Kaduna da hana raba kayan karatu
  • Jam'iyyar ta ce gwamna Uba Sani ya ki ya haɗa kai da sauran wakilai don inganta rayuwar al’ummar Kaduna, inda ya siyasantar da komai
  • Mataimakin mai magana da yawun PDP na kasa ya zargi wasu ‘yan siyasa da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu don biyan buƙatarsu
  • Yusuf Dingyadi, ya ce ‘yan majalisar PDP sun fi na jam'iyyar APC aiki, yana mai cewa ba za su bari a rushe nasarorin su da yaɗa ƙarya ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa babu wani ɗan Arewa mai hankali da zai mara wa APC baya a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'APC suka yi wa aiki': PDP ta fallasa asirin yan siyasar da suka bar jam'iyyar a Kaduna

PDP ta bayyana hakan ne a matsayin martani ne kan zargin rashin iya aiki da aka yi wa Sanata Lawal Adamu, mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya.

Jam'iyyar PDP ta magantu kan zaben 2027 da makomar APC a Arewa
Jam'iyyar PDP ta kare sanatan Kaduna, ta fadi makomai APC a zaben 2027 a Arewa. Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

PDP ta caccaki gwamnatin Kaduna

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa PDP ta kuma yi martani ga zargin da ake yiwa gwamnatin Kaduna na dakatar da rarraba kayan koyarwa da dan majalisar ya saya da kudade masu yawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yusuf Dingyadi, mai tallafawa shugaban PDP na ƙasa kan watsa labarai, ya ce akwai bukatar gwamnan jihar ya cire adawa, ya ya yi aiki tare da sauran wakilan al’umma don amfanin Kaduna.

"Abin da ake so shi ne gwamnati za ta yi aiki tare da sauran ‘yan siyasa don inganta rayuwar jama’a ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba," in ji Dingyadi.

Ya zargi wasu ‘yan siyasa da ɗaukar nauyin batanci da aikata ta’annati don faranta wa Shugaba Bola Tinubu da nufin cimma burinsu a 2027.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi babban rashi, ƙusa a jam'iyyar Kwankwaso ya koma APC

'Babu mai hankalin da zai zabi APC' - Dingyadi

Jam'iyyar PDP ta gargadi gwamnan Kano kan yadda yake tafiyar da mulki
PDP ta ba gwamnan Kaduna shawarar yadda ya kamata ya mu'amalanci 'yan adawa. Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Yusuf Dingyadi ya shaida cewa:

“Babu ɗan Arewa mai hankali da zai mara wa APC baya. Wasu ‘yan siyasa na nuna goyon baya ne kawai don biyan buƙatarsu, ba wai suna tare da shi da gaske ba."

Dingyadi ya yi gargaɗi ga Gwamna Uba Sani da kada ya bari wasu ‘yan siyasa da ya kira ‘'yan burga’ su ruɗe shi, yana mai cewa hakan zai iya zama barazana ga siyasarsa.

Ya jaddada cewa ‘yan majalisar PDP na aiki tukuru a mazabunsu fiye da na APC, yana mai cewa ba za su bari a rushe nasararsu ta siyasa ba.

“Ba za ku iya rushe nasararmu ta siyasa ba ta hanyar ɗaukar nauyin ƙaryace-ƙaryace ko shirya sauya sheka da nufin raunata jam’iyyarmu."

- Yusuf Dingyadi.

Sanatan Kaduna zai raba tallafin N500m

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Lawal Adamu Usman ya ware Naira miliyan 500 domin tallafawa Musulmai a mazabar Kaduna ta Tsakiya a lokacin Ramadan.

Sanata Lawal Usman ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci da sauran kayayyaki, domin saukaka wahalar da jama’a ke fuskanta a bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.