'A Gyara': Minista Ya Yi Barazanar Ficewa daga APC kan Shugabancin Jam'iyyar a Kano

'A Gyara': Minista Ya Yi Barazanar Ficewa daga APC kan Shugabancin Jam'iyyar a Kano

  • Sabon Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Ata ya yi barazanar ficewa daga APC idan har aka bar Abdullahi Abbas a matsayin shugabanta a Kano
  • Ata ya ce APC ta sha kaye a 2023 saboda kalaman shugabanninta da suka saba wa kudirar Allah
  • Ministan ya ce ba kuri’a ko kudi ke kawo mulki ba, sai Allah ya yarda inda ya ce idan ta ci gaba da rike na yanzu shugabanninta zai fice daga jam’iyyar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sabon Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Ata, ya yi barazanar ficewa daga jam’iyyar APC.

Yusuf Ata ya ce idan har jam'iyyar ta bar Abdullahi Abbas ya ci gaba da rike mukaminsa a matsayin shugabanta a Kano zai watsar da ita.

Minista ya koka kan tsarin shugabancin APC a Kano
Ministan gidaje da raya birane, Yusuf Ata ya yi barazanar ficewa daga APC. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Minista ya koka kan shugabancin APC a Kano

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Ata ya fadi haka a wani taron APC a karamar hukumar Fagge, Kano inda ya ce jam’iyyar ta fadi zaben 2023 ne saboda kalaman shugabanta da suka “kalubalanci ikon Allah", cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Kakakin Majalisar Kano ya ce da shugabannin APC sun yi hakuri, jam’iyyar za ta yi nasara, domin ikon Allah ne ke ba da mulki.

Ministan ya ce idan har jam’iyyar ta bar shugabanninta a kan mulki, to lallai APC ta shirya faduwa a gaba.

Minista ya caccaki tsarin shugabancin APC a Kano
Minista Yusuf Ata ya ce za su watse a APC idan ba a yi gyara kan shugabancinta ba a Kano. Bayo Onanuga, Yusuf Abdullahi Ata.
Asali: Twitter

Kano: Minista ya yi gargadi ga shugabannin APC

Ata ya ce:

“Muna sanar da kowa, idan suka dawo da su, za mu fice, kuma jam’iyyar za ta sake faduwa.”
“Ina tabbatar muku, ba za mu yarda da irin wadannan mutane ba. Suna turo mu da sako, muna mayar da martani.”
“Mun taso da tarbiyya, mun san Allah, muna girmama malamai da dattawa, ba za mu yarda a tauye mu ba.”

Kara karanta wannan

Me ya yi zafi? APC ta sanar da ficewa daga zaben ƙananan hukumomi, ta jero dalilai

“Na rantse da Allah, idan suka dawo da su, za mu bar jam’iyyar, kuma tabbas za ta sake rushewa."

Ya kara da cewa:

“Ba kuri’a ke ba da mulki ba, ba kudi ke saya ba, ba mazauna kasa ke bayarwa ba, sai dai Allah.”

Ata ya fadi aihnin wanda ya ci zaɓen Kano

Ata ya ce APC ta yi imani cewa Gawuna da Garo sun ci zaben 2023, amma an murde sakamakon, kuma kotu ta tabbatar an yi musu rashin adalci.

Ya ce:

“Duk da haka, Mai ba da mulki bai ba mu ba, domin mun kalubalanci ikonsa."

A halin yanzu, Abbas yana kan wa’adinsa na uku a matsayin shugaban APC a Kano.

Minista Ata ya yi bayan kan nada shi mukami

A baya, kun ji cewa Sabon karamin ministan gidaje da ci gaban birane, Yusuf Abdullahi Ata, ya ce burinsa shi ne dawo da Kano ga jam'iyyar APC a 2027.

Kara karanta wannan

"Za mu kawo karshen mulkin kama karya," PDP ta musanta baraka a cikinta

Lokacin ziyararsa ta farko a Kano bayan rantsar da shi, Yusuf Ata ya bayyana cewa nadinsa na da muhimmanci wajen karfafa APC.

Ata ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, inda ya jaddada kudurinsa na ciyar da APC gaba a Kano ta hanyar ziyartar jihar duk da tarin aikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.