2027: El Rufai Ya Fadi Yankin da Ya Dace Ya Hada Kai da Arewa domin Ceto Najeriya
- Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya sake yin magana kan zaben 2027 da kuma hanyar ceto Najeriya daga halin da take ciki
- Nasir El-Rufai ya ce dole ne Arewa ta hada kai da yankin Kudu maso Kudu don ceto Najeriya daga matsalolin da take fuskanta da kullum ke kara yawa
- Ya jaddada cewa Arewa da Kudu maso Kudu sun yi hadin gwiwa a baya, kuma yana da muhimmanci a koma ga wannan tsarin siyasa
- Wannan na zuwa ne bayan El-Rufai ya yabawa Atiku Abubakar inda ya ce ya taka rawar gani wajen kawo ci gaban tattalin arziki a mulkin Obasanjo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Kaduna - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya magantu kan hanyar ceto Najeriya daga mummunan halin da take ciki.
El-Rufai ya bayyana cewa dole ne yankin Arewa ya kulla kawance da Kudu maso Kudu don ceto kasar kamar yadda aka saba a can baya.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar

Asali: Facebook
El-Rufai ya yabawa Atiku kan kokarinsa a gwamnati
El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a 21 ga watan Faburairun 2025 yayin ziyarar ta’aziyya ga iyalan Edwin Clark, cewar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marigayi Clark wanda tsohon jigo ne a yankin Neja Delta kuma dattijo ya rasu a ranar 17 ga watan Fabrairun 2025 bayan fama da jinya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shi ya jagoranci tawagar domin yin ta'aziyya ga iyalan dattijon kuma tsohon minista.
Yayin ziyarar, El-Rufai ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya taka rawar gani wajen kawo ci gaban tattalin arziki a zamanin Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.
Ya ce mutane suna yawan manta alherin mutum sai dai idan ya yi wani kuskure ake ta yadawa inda ya ce hakan watakila dabi'ar dan Adam ne wurin manta alheri.

Asali: Twitter
El-Rufai ya ba da shawara kan hanyar ceto Najeriya
El-Rufai ya ce tun a shekarun 1960, 1970 da 1980, Arewa na da alaka mai karfi da Kudu maso Kudu a siyasa.
Ya ce wannan hadaka ya samar da abubuwan ci gaba a siyasar Najeriya gami da ceto kasar da kuma inganta wasu bangarori.
El-Rufai ya ce:
“A wancan lokaci, hadin kan siyasa tsakanin Arewa da Kudu maso Kudu yana da karfi. Kada mu manta da hakan. Mu koma ga wannan tsari. Dole ne mu ceci wannan kasa.
Siyasar 2027: El-Rufai ya gana da shugabannin PDP
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gana da shugabannin PDP a Kaduna sirrance, abin da ya tayar da jita-jitar ficewarsa daga APC kafin zaɓen 2027.
Wasu ‘yan Najeriya na ganin matakin Nasir El-Rufai wata dabara ce game da Gwamna Uba Sani, yayin da wasu ke fassara shi a matsayin sauya tsari.
Wannan na zuwa ne yayin da ake hasashen El-Rufai na shirin barin jam'iyyar APC duba da yawan ganawa da yake yi da jam'iyyun adawa a Najeriya.
Asali: Legit.ng