'APC Suka Yi Wa Aiki': PDP Ta Fallasa Asirin Yan Siyasar da Suka bar Jam'iyyar a Kaduna

'APC Suka Yi Wa Aiki': PDP Ta Fallasa Asirin Yan Siyasar da Suka bar Jam'iyyar a Kaduna

  • Shugaban jam'iyyar PDP na Kaduna, Edward Masha, ya yi tone-tone kan wadanda suka sauya sheka zuwa APC
  • Masha ya ce wasu 'ya'yan jam'iyyar da suka koma APC sun yi wa jam'iyyar aiki a 2023 don kayar da PDP a zabe
  • Ya bayyana cewa sauyin shekar ba zai hana PDP samun nasara a 2027 ba, domin jam’iyyar na da tushe mai karfi a matakin ƙasa
  • Shugaban jam'iyyar ya ce wasu sun bar jam'iyyar ne saboda rashin nasara a zabukan fidda gwani, amma PDP ba za ta lamunci cin amanarta ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Shugaban jam'iyyar PDP na Jihar Kaduna, Edward Masha, ya zargi wasu daga cikin mambobinsu da suka koma jam'iyyar APC da cin amana.

Masha ya ce mafi yawansu sun yi aiki ne domin jam'iyyar PDP nasara a zaben shekarar 2023 da ta gabata.

Kara karanta wannan

"Za a kayar da Tinubu": Kwankwaso ya hango wanda zai ci zaben shugaban ƙasa a 2027

Shugaban PDP ya tona asirin wadanda suka koma APC a Kaduna
Shugaban PDP a Kaduna ya caccaki waɗanda suka koma APC a Kaduna. Hoto: @ubasanius.
Asali: Twitter

PDP ta caccaki waɗanda suka sauya sheka

Masha ya yi wannan jawabi ne a taro da Kungiyar 'Yan Jarida ta Kudancin Kaduna a Zonkwa, hedikwatar Karamar Hukumar Zango Kataf, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar da cewa sauya shekar ba zai hana PDP nasara a 2027 ba, domin jam’iyyar na da tushe mai ƙarfi a matakin ƙasa.

Masha ya ce:

"Mutanen Kudancin Kaduna sun san wanda za su zaɓa, kuma za su duba ayyukan ‘yan takara."
PDP a Kaduna ta caccaki waɗanda suka sauya sheka
Shugaban PDP a Kaduna, Edward Masha ya tona asirin wadanda suka koma APC. Hoto: Edward Percy Masha.
Asali: Facebook

PDP ta sha alwashin nasara a zabe

Ya bayyana cewa a zaɓukan ƙasa, musamman Majalisar Dattawa da masu neman tazarce, tambayar da jama’a za su yi ita ce me suka yi wa al’umma?

Daga bisani, ya tabbatar da cewa PDP ta yi ayyuka nagari kuma za ta ci gaba da yin haka.

“Akwai dalilai da dama da ke sa mutane canza jam’iyya, idan ka rasa goyon bayan jama’a ko tsarin raba kujeru bai amfane ka ba, kana iya barin jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

"Ina mai tabbatar da cewa wasu daga cikin masu sauya shekar sun riga sun yi aiki da wata jam’iyya tun bayan faduwar su a zabukan fidda gwani na 2022.
"Mun san wannan kuma muna kallon hakan a matsayin cin amanar jam’iyya, ba za mu yi shiru ba; za mu yi amfani da doka don kare hakkokinmu."
"Idan ka duba tarihi, za ka ga waɗanda suka bar jam'iyyar ba su da wani tasiri a PDP, muna da tsari kuma za mu gudanar da zabukan fidda gwani.
"A zaben kananan hukumomi, PDP ta jagoranci tafiya bisa doka, yayin da APC ba ta gudanar da sahihan zabe ba a duk fadin Kaduna, a zabukan kasa, ba za su iya yin hakan ba. Wasu sun bar PDP don samun tikitin takara a wata jam’iyya, amma za su dawo."

- Cewar Edward Masha

Tinubu ya ba Sanata Sulaiman Hunkuyi mukami

Kun ji cewa kwanaki biyar bayan komawa APC, tsohon sanatan Kaduna, Suleiman Hunkuyi, ya samu nadin mukami a gwamnatin tarayya.

Sanata Hunkuyi ya damu muƙamin ne a Hukumar Ayyukan Majalisa (NASC) da ke wakiltar Arewa maso Yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.