Bidiyon Yadda Akpabio Ya Yi Wa Saraki Rashin Kunya a 2018 Yadda Aka Yi Masa a Majalisa

Bidiyon Yadda Akpabio Ya Yi Wa Saraki Rashin Kunya a 2018 Yadda Aka Yi Masa a Majalisa

  • A ranar 17 ga Oktoba, 2018, Godswill Akpabio da Bukola Saraki sun samu sabani kan yadda aka tsara wurin zama a zauren majalisar dattawa
  • Rikicin ya fara ne lokacin da Akpan ya zargi APC da shirin haddasa rikici a zaben gwamna na 2019 inda Akpabio ya nemi amsawa amma Saraki ya hana shi
  • Daga baya, Akpabio ya bukaci Saraki ya yi murabus daga shugabancin majalisa, yana mai cewa APC ce ke da rinjaye a zauren majalisar dattawa
  • Wannan ya biyo bayan rigima kan wurin zama da sake faruwa tsakanin Sanata Natasha da shugaban majalisar a yanzu, Godswill Akpabio

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Bayan samun hayaniya a majalisa kan wurin zama, an bankado yadda irin haka ya faru a 2018.

A ranar 17 ga Oktoba, 2018, Godswill Akpabio ya samu sabani da Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa a lokacin, kan yadda aka tsara wurin zama.

Kara karanta wannan

Rai ya yi halinsa: Tsohon sanatan Bauchi ya rasu a Abuja, an shirya jana'izarsa

An bakando bidiyon rigimar Akpabio da Saraki a 2018
Bidiyon yadda Akpabio ke ta da jijiyoyin wuya a majalisa ga Bukola Saraki a 2018. Hoto: Godswill Obot Akpabio, Bukola Saraki.
Asali: Facebook

Natasha, Akpabio sun rikita majalisar dattawa

Channels TV ta ce sabanin tsakanin Akpabio, sanatan Akwa Ibom da Saraki ya haddasa hatsaniya a zauren majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Alhamis 20 ga watan Faburairun 2025 wani sabon rikici ya barke tsakanin Akpabio da Natasha Akpoti-Uduaghan kan tsarin wurin zama.

Daga bisani, Akpabio ya ja kunnen Natasha inda ya bukaci a fitar da ita daga Majalisa saboda rashin bin doka.

Hakan ya jawo ka-ce-na-ce a tsakanin al'umma inda wasu ke goyon bayan Natasha yayin da wasu ke cewa ta karya doka kuma ba ta mutunta dokokin majalisar ba.

Natasha da Akpabio sun ta da kura a majalisar dattawa

Musabbabin rikicin Akpabio da Sanata Saraki

Rikicin a 2018 ya fara ne lokacin da Albert Akpan, sanatan Akwa Ibom ya zargi APC da shirin haddasa tashin hankali a zaben 2019.

Akpabio ya nemi yin magana ta amfani da abin magana na Ali Ndume, sanatan Borno ta kudu, saboda na kujerarsa ba ya aiki.

Kara karanta wannan

Mutuwa mai yankan kauna: Fitaccen basarake ya rasu, Tinubu ya jajantawa al'umma

Amma Saraki ya bukaci Godswill Akpabio ya koma wata kujera da ke da abin magana mai aiki.

Saraki ya ki amincewa da Akpabio ya yi magana ta amfani da abin magana na Ndume, lamarin da ya haddasa hatsaniya a majalisa.

Sakataren majalisa ya ce an rarraba wa Akpabio kujera da ke da abin magana mai aiki, amma sanatan ya ce ya fi son zama a wadda ba ya aiki.

Bayan taron, Akpabio ya bukaci Saraki da ya yi murabus daga shugabancin majalisa, yana mai cewa APC ce ke da rinjaye.

Lamarin ya faru ne bayan wasu watanni da Akpabio ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Sanata Akpabio ya sha alwashin kwace jihohi

Kun ji cewa Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce APC za ta lashe dukkanin jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027.

Akpabio ya ce zaɓen Monday Okpebholo a matsayin gwamnan Edo ya kasance hukuncin Allah don kawo sauƙi ga jama’ar jihar.

Hakan ya biyo bayan nasarorin da jam'iyyar APC ke samu a wasu jihohi bayan babban zaben 2023 da aka gudanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.