"Za a Kayar da Tinubu": Kwankwaso Ya Hango Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Ƙasa a 2027

"Za a Kayar da Tinubu": Kwankwaso Ya Hango Wanda Zai Ci Zaben Shugaban Ƙasa a 2027

  • Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce NNPP za ta samu nasara idan har aka shirya zaɓe cikin adalci da gaskiya a 2027
  • Kwankwaso ya bayyana haka ne a wurin taron majalisar zartarwa (NEC) ta jam'iyyar NNPP a Abuja ranar Alhamis
  • Ya buƙaci shuggaannin NNPP a dukkan matakai su tashi tsaye su yi duk mai yiwuwa don nasarar jam'iyyar a zaɓe mai zuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jagoran NNPP na ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa za ta yi nasara a zaɓen 2027 idan an gudanar da shi cikin adalci da gaskiya.

Kwankwaso ya yi wannan furuci ne a taron majalisar zartarwa ta jam’iyyar (NEC) karo na takwas da aka gudanar a Bolingo Hotel, Abuja, a ranar Alhamis.

Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya bayyana kwarin gwiwar cewa NNPP za ta yi nasara a zaben 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Twitter

Kwankwaso ya caccakin mulkin APC

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

A yayin jawabin nasa, ya soki jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa ta kara ta’azzara talauci da rashin tsaro a kasar nan, kamar yadda Leadership ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matsalar tattalin arziki, rashin tsaro, da tabarbarewar ababen more rayuwa, musamman a Arewacin Najeriya, sun tilasta wa mutane rayuwa cikin fatara da ƙunci.

Kwankwaso ya bukaci 'yan Najeriya da su yi tunani kan halin da suke ciki sannan su ba NNPP dama na jagoranci kasar nan a zaɓe na gaba.

Kwankwaso na da ƙwarin gwiwa a 2027

“Muna sane da irin matsalolin da APC da PDP ke fuskanta. Idan aka gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci, NNPP za ta kayar da APC, PDP da sauran jam’iyyu,” in ji Kwankwaso.

Ya kuma yi magana kan matsalolin cikin gida da NNPP ke fuskanta, yana mai cewa ikirarin wasu korarrun ƴan jam’iyyar ba komai ba ne face ƙoƙarin karkatar da hankali.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi babban rashi, ƙusa a jam'iyyar Kwankwaso ya koma APC

Kwankwaso ya tabbatar wa mambobin jam’iyyar cewa yana aiki tare da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) don ƙarfafa dimokuradiyya a Najeriya.

NNPP na bukatar haɗa kan ƴaƴanta

Ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su kasance tsintsiya maɗaurinki ɗaya tare da mai da hankali wajen cin nasara a zaɓen 2027, The Cable ta rahoto.

“Zan ci gaba da yin duk abin da ya dace domin nasarar jam’iyyarmu. Ina roƙon shugabanninmu daga jihohi, kananan hukumomi da mazabu da su dage don ganin NNPP ta yi nasara a 2027,” in ji shi.
Kwankwaso a taron NNPP.
Kwankwaso ya nemi haɗin kan ƴan NNPP gabanin 2027 Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Kano ta ɗauki ilimi da muhimmanci

A nasa bangaren, Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa Abdulsalam Aminu Gwarzo ya wakilta, ya jaddada cewa gwamnatin Kano ta fi mai da hankali kan ilimi da bunƙasa walwalar jama'a.

Ya ce Kano ta ware kashi 31% na kasafin kuɗin ta na 2024 ga bangaren ilimi, wanda ya fi kowace jiha a Najeriya, abin da ke nuna NNPP na da kyakkyawar manufa a fannin ilimi.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

“Muna alfahari da abin da ke faruwa a Kano. Ilimi ga kowa shi ne taken jam’iyyarmu, kuma babu wata jiha da ta kai mu yawan abin da muka cimma,” in ji gwamnan.

Wani ɗan Kwankwasiyya, Saidu Abdu ya shaidawa Legit Hausa cewa tuni suka fara shirye-shiryen tunkarar zaben 2027.

Ya ce sun da ƙwarin guiwar cewa ƴan Najeriya za su yi wa kansu karatun ta natsu, su gane cewa ba abin da APC za ta iya yi na ceto kasar nan da matsi.

Jigon NNPP ya ce:

"Maganar mai gida haka take, idan ka duba ko a 2023, APC ta sha wahala sai da ta yi amfani da makirci da kudi sannan ta kai labari.
"Wani lokacin ba mu hangen wuya sai mun tsinci kanmu a ciki, ni na san indai mutane za su saka kowane ɗan takara a sikeli, ba tantama Kwankwaso zai ci zaɓe."

Kwankwaso ya gana manyan kusoshi

Kara karanta wannan

"Za mu kawo karshen mulkin kama karya," PDP ta musanta baraka a cikinta

A wani rahoton, kun ji cewa Kwanwaso ya fara tuntuɓar manyan ƴan siyasa a Najeriya a wani ɓangare na shirye-shirye sake neman takara a 2027.

An ga Kwankwaso ya gana da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, El-Rufai da tsohon shugaban ƙasa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel