Kwana 5 da Komawa APC, Tinubu Ya Nada Tsohon Sanatan Kaduna Mukami a Gwamnatinsa
- Kwanaki biyar bayan komawa APC, tsohon sanatan Kaduna, Suleiman Hunkuyi, ya samu nadin mukami a gwamnatin tarayya
- Sanata Hunkuyi ya damu muƙamin ne a Hukumar Ayyukan Majalisa (NASC) da ke wakiltar Arewa maso Yamma
- Tsohon Sanatan ya bar APC ne bayan da ya saba da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, kan rancen kudin waje
- Wasu sun ce Hunkuyi na canza jam’iyya idan bai gamsu da gwamnati ba, don haka yana iya barin APC nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Kwanaki biyar bayan komawarsa jam'iyyar APC, tsohon sanatan Kaduna, Suleiman Hunkuyi, ya samu mukami.
An nada Hunkuyi a matsayin wakilin Arewa maso Yamma a Hukumar Ayyukan Majalisar Tarayya (NASC).

Asali: Facebook
Sanata Hunkuyi ya koma jam'iyyar APC
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Dada Olusegun ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar 16 ga Fabrairun 2025, Gwamna Uba Sani ya karɓi wasu ‘yan adawa 50 da suka dawo APC, ciki har da Sulaiman Hunkuyi, Shehu Sani da tsohon gwamna Ramalan Yero.
Hunkuyi ya rike kujerar sanatan Kaduna ta Arewa tsakanin 2015 zuwa 2019 a APC kafin barinta.
Ya bar jam'iyyar bayan ya hada kai da wasu sanatoci daga jihar wajen adawa da bukatar Gwamna Nasir El-Rufai na rance daga waje.
A zaben fidda gwani na APC na 2019, Abdu Kwari ne ya karbi tikitin takarar Hunkuyi.
Sanata Shehu Sani ma ya rasa tikitinsa na komawa majalisar dattawa ga Gwamna Uba Sani.
Yadda Hunkuyi ya rika sauya sheka daga jam'iyyu
A 2023, Hunkuyi ya tsaya takarar gwamnan Kaduna a NNPP, tarihinsa ya nuna yana canza jam’iyya idan bai gamsu da gwamnati ba.
A 2003, ya sauya sheka zuwa ANPP don yin takara da tsohon abokinsa, Gwamna Ahmed Makarfi.

Kara karanta wannan
'Ba shi da tsoro ko kadan': Abin da Tinubu ya ce bayan babban rashin da Najeriya ta yi
Daga baya ya koma PDP bayan yin tafiya a CPC da APC, komawarsa APC na nufin ya hade da gwamnati mai ci.
Uba Sani: Sanata Hunkuyi ya shawarci El-Rufai
A baya, kun ji cewa Sanata Suleiman Othman Hunkuyi ya shawarci tsohon gwamna Nasir El-Rufai da ya amince da Gwamna Uba Sani a matsayin jagora a Kaduna.
Sanata Hunkuyi ya bukaci El-Rufa’i da ya nemi gafarar Allah da kuma bai wa mutanen Kaduna hakuri kan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa.
Asali: Legit.ng